Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ɗage sauraron ƙarar zargin almundahanar da EFCC ke yi wa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, zuwa 21 ga watan Janairun 2025.
A zaman kotun a ranar Laraba, lauyan EFCC, Kemi Pinheiro SAN, ya ce yana da shaidu biyu da zai gabatar, sannan ya buƙaci kotun ta ci gaba da karɓar shaidu ba tare da wanda ake zargi ba ya amsa ko ya musanta zargin da ake masa ba.
Pinheiro ya ƙada da cewa, “haƙƙin amsa laifi ko musantawa ba dole ba ne, dama ce da za a iya ƙwacewa,” in ya ce wanda suke ƙara ya yi watsi da damarsa.
A nasa ɓangaren wanda ake ƙara, lauyansa, Michael Adoyi ya ce bai amince da wannan ba, inda ya ce buƙatar lauyansa masu ƙara ta ci karo da wani hukuncin kotun da ake dako.
A ƙarshe sai alƙalin kotun, mai shari’a Nwite ya ce ba zai yiwu ba a yanke hukuncin shari’ar a bana, sai ya ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa 21 ga watan Janairun 2025.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 11 hours 51 minutes 54 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 33 minutes 19 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com