Tinubu ya ba da umarnin sakin yaran da aka gurfanar a kotu kan zanga-zanga

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin sakin dukkan ƙananan yaran da aka kama da zargin cin amanar ƙasa sakamakon shiga zanga-zanga kan tsadar rayuwa.

Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya ce an kuma kafa wani kwamati da zai bincika yadda aka kama su, da tsarewa, da kuma kula da su.

“Shugaban ƙasa ya ce a sake su kuma a sadar da su ga iyayensu,” in ji ministan lokacin da yake magana manema labarai a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Bayanan sun fito ne jim kaɗan bayan kammala rantsar da sababbin ministoci bakwai da Shugaba Tinubu ya naɗa a fadarsa a yau Litinin.

A cewar ministan, umarnin ya shafi dukkan yara a faɗin ƙasar, sannan kuma kwamatin zai yi aikin zai kasance ƙarƙshin ma’aikatar agaji da rage talauci, in ji ministan.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 8 hours 36 minutes 35 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 10 hours 18 minutes 0 second

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com