Taron G20 ya sake fito da damar haɗin kan duniya don kawar da yunwa da talauci – Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce tattaunawar da aka yi a taron G20 a Brazil, ta sake bayyana babbar damar haɗin kai tsakanin ƙasashe don tunkarar ƙalubalen da duniya ke fuskanta gaba ɗaya.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinta na Facebook bayan gabatar da jawabi a taron, Shugaba Tinubu ya ce a taron G20 na bana, Najeriya ta amince da yunƙurin shugaban ƙasar Brazil na neman haɗin kan duniya domin kawar da babbar barazanar da duniya ke fuskanta, wato yunwa da talauci.

”Wannan ƙuduri ya yi daidai da muradin Najeriya na yaƙi da yunwa da talauci, da samar da ci gaba mai ɗorewa ta hanyar samar wa ‘yan Najeriya ayyukan yi”, in ji shi.

Shugaban na Najeriya ya sake jaddada shawarar ƙasashen Afirka na sake fasalin cibiyoyin duniya, ciki har da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ƙungiyar G20, don tabbatar da adalci da tafiya da kowa ta yadda Najeriya da ƙasashen Afirka za su shiga a dama da su wajen ɗaukar matakai a waɗanann cibiyoyi.

”A kan sauye-sauyen tattalin arziki, na jaddada ƙudurin Najeriya na tabbatar da adalci a tsarin haraji na duniya da tsarin hada-hadar kuɗi wanda zai cike giɓin da ke tsakanin manyan da ƙananan ƙasashen duniya”.

Shugaba Tinubu ya kuma a yayin da gwamnatinsa ke neman faɗaɗa haraji ta Najeriya ba tare da ƙara wa ‘yan ƙasa wahala ba, gwamnatin ta mayar da hankali kan rage wahalhalu da ɓullo da ƙarin damarmaki da inganta ayyukan more rayuwa, da ƙarfafa ilimi da cibiyoyin tsaro da zamantakewa, waɗanda ya ce suna da mahimmanci don sake farfaɗo da ci gaban ƙasar.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1255 days 3 hours 38 minutes 23 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1237 days 5 hours 19 minutes 48 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com