Hukumar Hisbah ta jihar Kano a Najeriya ta ce za ta ci gaba da bin tsarinta na rufe shagunan masu caca bayan hukunci wata kotu.
A ranar Juma’a kotun ƙolin ƙasar ta rushe dokar 2005, da ta amince da kafa hukumar kula da caca tare da halasta cacar wasanni a ƙasar.
Kotun ta ce hukuncin na nufin gwamnatocin jihohi ne ke da wuƙa da nama game da dokokin da suka shafi caca.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Daraktan hukumar Hisbah na jihar Kanon, Dakta Abba Sufi ya ce hukuncin kotun na nufin hukumarsu za ta ci gaba da kai samame tare da rufe shagunan caca a faɗin jihar, saboda haramcin sana’ar a ƙarƙashin dokokin Musulunci.
Abba Sufi ya ce iyayen yara na yawan ƙorafi game da yadda yaransu ke ci gaba da faɗawa komar wannan mummunar sana’a a daidai lokacin da matsin rayuwa da talauci ke ƙaruwa tsakanin al’umma.
Jihar Kano na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya da ake amfani da dokokin addinin Musulunci baya da dokokin ƙasa.
A watan da ya gabata hukumar Hisbar jihar ta kai samame tare da rufe gomman shagunan caca a faɗin birnin Kano.
To sai dai an dakatar da samamen sakamakon ƙarar da wasu ƙungiyoyi suka shigar, dogaro da cewa caca ba laifi ba ne a ƙarƙashin dokokin Najeriya.











