NAHCON ta bayyana dalilian da suka saka Saudiya rage mata kujerun aikin hajji bana

Hukumar Alhazan Najeriya ta bayyana damuwarka kan matakin da hukumomin Saudiyya suka ɗauka na rage wa ƙasar wani kaso mai yawa na kujerun aikin Hajjin da aka ware mata.

NAHCON ta yi gargaɗiin cewa matakin zai hana mutane da dama zuwa aikin Hajjin a shekara mai zuwa.

Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar ranar Alhamis, ta ce hukumomin Saudiyya sun sanar da NAHCON cewa wuraren kwanan mutum 66,910 kawai aka keɓe wa ƙasar, wani abu da ke nuna adadin maniyyatan da aka ware wa Najeriyar.

“Wuraren kwanan da aka keɓe wa maniyyatan Najeriya a 2026 shi ne 66,910, da suka haɗa da na hukumomin alhazai na jihohi 51,513 da sauran jami’an hukumar, yayin da aka ƙebe wurare 15,397 ga kamfanonin shirya tafiye-tafiye”, in ji sanarwar.

Hukumar ta NAHCON ta ce hukumomin Saudiyyar sun ɗauki matakin ne saboda Najeria ta kasa cike kujeru 95,000 da aka ware mata a shekarar 2025.

NAHCON ta ce a shekarar da ta gabata an samu kujeru 35,872 da ba a cike su ba.

Ƴan ƙasar da dama sun alaƙanta rashin cike kujerun da tsadar kuɗin hajjin da aka samu a 2025.

Matakin Saudiyyar na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya umarci hukumar NAHCON ta rage kuɗin aikin hajjin 2026.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com