Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta ɗauki matakin gaggawa wajen nazari tare da gyara harkokin tsaron sararin samaniyar ƙasar domin daƙile amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare a ƙasar.
Zulum ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a garin Mafa bayan wani hari da ƴan Boko Haram suka kai kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
“Babban abin da nake so in yi magana a nan shi ne amfani da jirage marasa matuƙa. An faɗa min cewa sun yi amfani da jirage marasa matuƙa a Dikwa. Wannan abin tashin hankali ne matuƙa.”
“Yawaitar jirage marasa matuƙa a hannun maƙiya abu ne mai matuƙar haɗari. Dole mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen daƙile wannan sabon salon,” in ji Zulum.
Gwamnan ya ce akwai buƙatar a ƙara tsaurara matakan kariya a bakin iyakokin ƙasar, “sannan akwai buƙatar a ƙara inganta tsaron sararin samaniyarmu. Wannan mataki ne da ya kamata a ɗauka cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba.”
Zulum ya yi kira ga al’ummar jihar da su riƙa ba jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar kai su bayana sirri da za su taimaka musu wajen magance matsalolin tsaro.
“Maganar gaskiya mun samu labarin za a kai hari a Mafa, kuma dukkan hukumomin da suka cancanci sani an faɗa musu. Wannan ne ya sa nake tunanin akwai zagon-ƙasa a harkar. Shi ya sa nake a zo a duba tare da yin gyara.”










