Gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi maraba da duk wani taimako daga Amurka kan magance masatsalar masu tayar da ƙayar baya, matsawar za a mutunta kimarta.
Mai magana da yawon shugaban ƙasar, Daniel Bwala ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi ya ce kamat yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito”Muna maraba da taimakaon Amurka wajen yaƙi da masu tayar da ƙaya baya a ƙasarmu matsawar za ta kare mutuncinmu”.
Shugaba Trump na Amurka ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Najeriya, idan hukumomin ƙasar ba su ɗauki mataki bakan abin da ya kira ”yi wa kiristoci kisan kiyashi a ƙasar”.
A ranar Lahadi ne Donald Trump ya shaida wa manema labarai cewa sojojin Amurka za su aika dakaru Najeriya ko su ƙaddamar da hare-hare ta sama domin dakatar da abin da ya kira ”kisan kiristoci a ƙasar”, sai dai bai bayar da cikakken bayani ba.











