Jagoran jam’iyyar NNPP a Najeriya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ƙaruwar hare-hare da ake samu na baya-bayan nan a ƙasar ya kai matakin da ke buƙatar matakin gaggawa daga hukumomi, musamman daga gwamnatin ƙasar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Kwankwaso ya ce wajibi ne gwamnatin Najeriya ta sauke babban nauyin da ke kanta na kare rayukan al’umma, ta hanyar ƙarfafa wa jam’ian tsaron ƙasar gwiwa.
”Da farko, sace ɗalibai ƴanmata 25 a Kebbi abin damuwa ne da ke sanya fargabar ko za a maimaita abin da ya faru a baya, sai sacewa da kuma kashe Birgadiya janar M Uba da ƴan ta’adda suka yi a Borno, wanda yana daga cikin lokuta mafi muni a yaƙin da ƙasar ke yi da ta’addanci,” in ji shi.
Ya kuma nuna damuwa game da sace gwamman mutane a Zamfara, da kuma ƙaruwar harin da ƴan bindiga ke kai wa a ƙananan hukumomin Shanono da Ghari a jihar Kano.
”Ina kira a yi gaggawar ceto waɗanda aka sace, domin hare-haren baya-bayan nan na nuna koma baya a yaƙin da ake yi da matsalar tsaro,” a cewar sa.











