An karrama Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA, da washu shuwagabnnin hukumomin tsaro a Nijeriya da lambar yabo.
Wannan na zuwa ne a yayin taron SEAMA karo na 7, tare da taron bayar da lambar yabo don tsaro da taimakon gaggawa (SEAMA 2025); a taron an karrama mayyana jamián tsaro bisa gudunmawar da suka bayar ga Al’uamma da kasa baki daya.
Taron da jaridar Emergency Digest, dake karkashin rukunin kafanin yada labarai na Image Merchants Promotion Limited – IMPR) bisa hadin gwiwar cibiyar dakile yaduwar rikice –rikice ta fannin sadarwa wato CCC, da CISLAC da kuma kungiyar TIEMS ya bayyana nasarorin da aka samu a shekarar da ta gabata.
A yayin taron shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyin Birgediya Janar Bubu Marwa mai ritaya ya rabauta da lamabar yabo da “fitaccen shugaba” bisa irin yadda ya jagorancin kawo sauye –sauye a fannin yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Nijeriya.
A karkashin jagorancinsa, hukumar NDLEA ta fatattaki ƙungiyoyin dillalan ƙwayoyi, ta ƙarfafa binciken leƙen asiri, tare da wayar da kai kan illolin ƙwayoyi karkashin shirin WADA.
ko dai a ‘yan tsakankanin nan shugaba Tinubu ya tabbatar da karin wa’adinsa na shekaru biyar bisa gudummawar da hukumar ta bayar wajen tsaro.
Daga cikin wadanda aka karrama, daraktan yada labaran hukumar ta NDLEA Femi Babafemi, matsayin “Fitaccen Jami’in Wayar da Kan Jama’a a Lokacin Rikici”. Bisa ayyukansa na wallafa bayanai, bayyana nasarorin kama miyagun ƙwayoyi da masu fatauci, da kuma gyara bayanan da ke rikita jama’a, domin tabbatar da sun ƙara inganta suna da sahihancin daga hukumar.
A watan Satumbar 2025, ya bayyana sakin wasu ‘yan Najeriya uku da aka tsare a kasar Saudiyya ba bisa ka’ida ba — abin da ya nuna jajircewarsa ga adalci da ingantacciyar sadarwa.
Sai kuma Kwamandan hukumar NSCDC na birnin Abuja, Olusola Odumosu, wanda ya sami lambar yabo ta “Jami’in Tsaro na Shekara” saboda kwazonsa wajen magance laifuka, kama masu fasa kwauri da masu barna a babban birnin tarayya.
Haka kuma, Kwamishinan ‘Yan Sanda na Legas, CP Olohundare Moshood Jimoh, ya samu lambar yabo ta “Jami’in ‘Yan Sanda na Shekara” saboda yadda ya tarwatsa manyan ƙungiyoyin laifi, musamman a Ikorodu da Shomolu, ta hanyar amfani da bayanan sirri don hana aikata laifi da kakkabe ayyukan ‘yan ƙungiya.
Read Also:
Kwamodo Omobamidele Adetokunbo Akinbami, Kwamandan NNS SOROH, shi ne “Jami’in Soja na Shekara” saboda yaki da fashin teku, lalata bututun mai, da karancin mai a jihohin kudanci. Daga Mayu 2024 zuwa Afrilu 2025, rundunarsa ta rushe haramtattun matatun mai guda 145, ta kama jiragen ruwa, ta kwato danyen mai da dizal da aka sace, tare da lalata sansanonin ‘yan bindiga a yankunan ruwa.
Daga cikin sauran mutanen da aka karrama akwai Rahila Lassa Garba daga Voice of Nigeria (VON), wadda ta samu yabo kan aikin jarida na jinƙai da yake fayyace halin da al’ummar da ke cikin mawuyacin hali ke ciki, tare da jawo daukar matakan tallafi.
A bangaren hukumomi kuwa, DSS ta samu lambar yabo kan “Magance Laifi”, yayin da Hukumar Kwastam (NCS) ta samu yabo kan “Gudanar da Bayanai da Wayar da Kan Jama’a” saboda yadda take fitar da bayanai cikin gaskiya da kauce wa yaɗuwar jita-jita. EFCC ta samu yabo wajen “Rigakafin Laifukan Sadarwa (Cybercrime)”, FRSC kan “Ceton Gaggawa”, yayin da Yobe SEMA ta samu yabo kan “Ayyukan Jinƙai”.
Sauran hukumomin da aka karrama sun haɗa da: Rundunar Sojin Najeriya (NA) saboda ayyukan CIMIC, ICPC saboda tsantseni wajen bincike, da NAF saboda inganta alaƙar soji da jama’a ta hanyar ayyukan jinƙai. Makarantar Horas da Ma’aikatan Gidajen Gyara Hali ta Kaduna ta zama “Makarantar Horaswa ta Shekara”.
Taron ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, kafafen yada labarai, da kungiyoyin farar hula wajen kare Najeriya da inganta wayar da kai ga jama’a. SAEMA 2025 ta nuna yadda karramawa kan nagarta ke ƙarfafa jajircewa wajen yaki da laifuka da kare rayuka.
PRNigeria










