Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin daurin rai da rai bisa samunsa da dukkan laifukan da ake tuhumarsa da su.
Kotun ta yanke masa hukuncin ne bayan samunsa da laifuka bakwai, waɗanda suke da alaƙa da ta’addanci da tunzura mutane.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a James Omotosho ya ce laifukan Kanu sun cancanci hukuncin kisa ne, amma ya ce kasashena ƙasashen duniya suna nuna rashin jin daɗi kan hukuncin kisa, sai ya mayar da hukuncin na ɗaurin rai da rai.
Read Also:
Sai dai alƙalin ya ce a nema wa Kanu wani gidan yarin daban ba na Kuje da ke Abuja saboda a cewarsa yana da hatsari, sannan ya haramta masa amfani da waya da sauran na’urorin sadarwa, inda ya ce idan ma zama dole sai ya yi, “to ya kasance ana sa masa ido sosai,” in ji alƙalin.
Tuhume-tuhumen da ake yi wa Kanu sun haɗa da ta’addanci da tunzura jama’a su kashe ƴansanda da sojoji da kasancewa mamba a haramtacciyar ƙungiyar IPOB da gwamnatin Najeriya ta haramta da kuma yaɗa farfagandar ta’addanci.










