Gwamnatin Jihar Kano ta sake tabbatarwa mazauna jihar cewa al’amuran tsaro suna tafiya yadda ya kamata, kuma babu wata barazana da ya kamata ta tayar da hankalin jama’a.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya PRNigeria a safiyar litinin.
Sanarwar ta kara da cewa gwamnan ya bayar da tabbacin ne bayan taron majalisar tsaron jihar da aka yi a ranar Lahadi tare da manyan jami’an tsaro, inda aka sake jaddada kudurin gwamnati na tabbatar da zaman lafiya a dukkan yankunan jihar.
Gwamnatin ta ce duk wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta na cewa akwai gagarumar barazanar tsaro a Kano, ba shi da tushe balle makama. Ta ce babu wani sahihin bayanan asiri da ke nuna akwai matsalar tsaro da ta taso ko ta gabatowa a jihar .
Read Also:
Sanarwar ta jaddada cewa gwamnati ba za ta lamunci yada bayanan ƙarya da nufin tayar da hankalin jama’a ba, tare da gargadin cewa irin wannan ɗabi’a na iya janyo hukunci daga hukumomi.
Gwamnatin ta bayyana cewa tana aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro, tare da tabbatar da cewa jami’an tsaro sun kasance cikin shiri, kuma an tura su muhimman wurare, suna aiki ba dare ba rana domin tabbatar da zaman lafiya a Kano .
Sanarwar ta kara da cewa an sanya dukkan sassan Kano cikin tsauraran matakan sa ido, tare da ingantaccen tsarin tsaro da ke aiki yadda ya kamata.
Gwamnatin ta roki jama’a su kwantar da hankalinsu, su guji yada jita-jita a kafafen sada zumunta. Ta kuma yi gargaɗin cewa masu yada labaran ƙarya su daina, domin hakan na iya jawo wa mai yi hukunci.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnati na kara inganta ayyukan leken asiri, haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, da kuma sabunta dabarun tsaro na zamani a fadin jihar Kano











