Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP, wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da rikicin cikin gida a jam’iyyar ke kara karuwa.
Adeleke ya sanar da hakan ne ta shafinsa na X a daren Litinin, inda ya wallafa kwafin takardar murabus dinsa mai dauke da kwanan wata 4 ga Nuwamba, 2025.
A cikin takardar, Adeleke ya bayyana rikicin da ke faruwa a jam’iyyar a matsayin dalilin ficewarsa.
Ya rubuta cewa: “Sakamakon rikicin da jam’iyyar ke fama da shi, na yanke shawarar ficewa daga cikinta daga yau.”
Gwamnan ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta bashi ya yi aiki a matsayin Sanata mai wakiltar Osun West (2017–2019) da kuma Gwamnan jihar Osun.
Adeleke dai bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba bayan barin PDP.











