Gwamnatin jihar Nasarawa ta bayyana shirinta na kafa rundunar ‘yan sandan jiha idan kundin tsarin mulkin ƙasar ya amince da hakan.
Kalaman sun fito ne daga kwamishinan tsaro da harkokin sauran al’amura, CP Usman Baba yayin wani taron manema labarai a Lafia, babban birnin jihar.
Kwamishinan ya ce tun daga zuwan gwamnatin jihar a 2019, an fifita harkar tsaro, tare da ba rundunonin tsaro tallafi na ababen hawa da kayan aiki da sauran kayan aikace-aikace.
Ya jaddada cewa gwamna Abdullahi Sule ya ƙuduri aniyar tabbatar da cewa jihar ta kasance amintacciya ga masu zuba jari da kuma wuri mai cike da zaman lafiya ga al’ummarta.
Haka kuma, ya bayyana cewa an tura jami’an tsaro zuwa makarantu a yankunan da ake ganin barazana ce, da manyan wuraren ibada a babban birnin jihar da kuma dukkan ƙananan hukumomi 13 na jihar.
Game da matsalar garkuwa da mutane, kwamishinan ya ce gwamnati na aiki tare da hukumomin tsaro, ‘yan sa kai da masu sa ido a unguwanni domin magance lamarin.
Ya gargadi masu aikata laifi cewa jihar za ta zama “wuri mai zafi” gare su, inda duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsanani.











