‘Yan uwan wata mata Aishatu Umar, sun koka kan yadda suke zargin likitoci a asibitin Abubakar Imam sun manta Almakashi a Cikin ‘yar’uwarsu, abin da yayi sanadiyyar mutuwarta.
Ta cikin wani rubutu a shafin facebook da Abubakar Muhammad, ɗan’uwa ga marigayiyar ya wallafa, ya zargi sakacin likitocin matsayin abin da yayi sanadiyyar mutuwarta.
Read Also:
Yace a watan Satumbar daya gabata ne, aka yiwa Aisha aikin tiyata a Asibitin ƙwararun na Abubakar Imam dake Kano, al’amarin da daga baya ha dinga haifar mata da matsanancin ciwon mara.
Bayan ƙorafe-ƙorafe da yace mariganyar ta yi ga likitocin asibitin lokuta da dama amman suna nuna ba wata matsala, sai daga baya suka yanke shawarar zuwa a ɗau gwajin hoton cikin, inda anan ne aka gane almakashin fiɗa aka bari a cikinta bayan tiyatar. Gano hakan ya faru ne kwanaki biyu kafin rasuwarta.
Sai dai bayan fitar labarin, hukumar dake lura da asibitocin jihar Kano ta bayar da umarnin gudanar da bincike akan lamarin.










