Yau sabbin dokokin shige da fice na Amurka, wanda Shugaba Donald Trump ya gabatar, na dakatar da aikace-aikacen bada bizar Amurka ga ƙasashe 75, ciki har da na Afirka 26, da suka haɗa da Ivory Coast da Kamaru da Senegal da kuma Najeriya za su fara aiki.
Tun a makon jiya Fadar White House ta sanar da matakin Amurka dakatar da bayar da bizar ƴan ci rani ga ƴan ƙasashe 75, a wani mataki da ta ce yana da nasaba da sake duba tsarin tantance masu neman shiga Amurka.
Read Also:
A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar, an umurci dukkan ofisoshin jakadancin Amurka da ke ƙasashe da lamarin ya shafa da su dakatar da bayar da irin waɗannan biza, sanarwar ta bayyana cewa dakatarwar za ta fara aiki ne cikin mako guda, wanda ke daidai wannan Laraba 21 ga watan Janairu, amma ba a fayyace tsawon lokacin da za a ɗauka kafin a janye ta ba.
Dakatarwar ta shafi biza iri-iri, na bakin haure da waɗanda ba bakin haure ba, tsabanin bizar yawon shaƙatawa, wannan mataki ya mayar da hankali kan tafiya Amurka don neman aiki ko karatu ko haɗuwar iyali.
Ba’a bayyana sunayen ƙasashen 75 da wannan sabon mataki ya shafa ba, amma majiyoyi sun ce dakatarwar ta shafi Rasha da Iran da Afghanistan da Thailand da Brazil da wasu ƙasashen Afirka, ciki harda Najeriya.
Ga shugaba Donald Trump, gwamnati da ɗauki wannan mataki ne domin aiwatar da sauye-sauye a fannin shige da fice, domin tabbatar da cewa baƙi sun kasance masu dogaro da kansu a fannin kuɗi, amma ba masu zama jidali ga Amurkawa ba.











