Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya cire Sunusi Surajo Kwankwaso daga mukamin mai ba shi shawara kan harkokin siyasa tare da maye gurbinsa da Mustapha Buhari Bakwana.
Hakan na cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran Gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Read Also:
Idan za’a iya tunawa Sunusi Surajo Kwankwaso ya bayyana cewa ya kai takardarsa ta ajiye aiki amma anki karbar, wanda ya ce hakan ce tasa a fito fili ya fadawa Duniya cewa ya ajiye mukamin nasa.
Sunusi Surajo Kwankwaso dai na daga cikin wadanda tun a tashin fari suka nuna cewa za su kasance tare da madugun Kwankwasiyya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Wannan dambarwar dai ta Sami asali ne tun lokacin da aka fara jita-jitar gwamnan Kano zai raba gari da ubangisansa na Siyasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Bakwana dai ya taba rike wannan mukamin lokacin mulkin Dr. Abdullahi Umar Ganduje yana gwamnan Kano.












