Home Taska ‘Yan Bindiga sun ƙone shingen Jami’an NSCDC Tare da Garkuwa da Mutum...

‘Yan Bindiga sun ƙone shingen Jami’an NSCDC Tare da Garkuwa da Mutum 1 a Jihar Kebbi

‘Yan Bindiga sun ƙone shingen Jami’an NSCDC Tare da Garkuwa da Mutum 1 a Jihar Kebbi

Wasu ’yan bindiga sun kai hari garin Tsamiya da ke Ƙaramar Hukumar Bagudo a Jihar Kebbi, inda suka ƙone shingen bincike na rundunar Sibil Difens (NSCDC), tare da lalata wasu gine-gine a yankin.

Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun kuma yi garkuwa da wani mutum mai suna Alhaji Yusuf Bazamfare yayin harin da suka kai a ranar Asabar.

A cewar mazauna yankin, ’yan bindigar sun kuma ƙone gidan karuwai da kuma gidan wani mutum mai suna Sule Mai Goge sannan suka tsere.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce rundunar ta tura jami’anta zuwa yankin nan take bayan samun rahoton harin.

Ya ce Kwamishinan ’yan sandan jihar ya bayar da umarnin tura ƙarin jami’an tsaro domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin.

“An fara bincike kan lamarin, sannan ana ƙoƙarin gano inda aka kai wanda aka yi garkuwa da shi domin kuɓutar da shi,” in ji shi.

SP Bashir Usman ya kuma buƙaci mazauna yankin da su kwantar da hankali tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gudanar da aikin ceto da bincike.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Haba, Abba Bichi — Waɗannan Tallace-Tallacen Ranar Haihuwa Sun Wuce Iyaka! Daga Yushau A. ShuaibNAF ta Kaddamar da Aikin Ceto Bayan Jirgin Saman Soja ya Fado a OndoSojoji Sun Kashe Mayakin B'Haram, Sun Kama Wani a GeidamRijistar Masu Kaɗa Kuri'a a Najeriya ta Kai Miliyan 103 - INECMuna Kafa Sabbin Sansanonin Sojoji Domin Kare Al'ummomin da ke Cikin Hatsari – TinubuJirgin Sojojin Sama (NAF) ya Fado a Ondo Dauke da Mutane 32Sojojin Najeriya Sun Kaddamar da Sabbin Bataliyoyi 3 Don Karfafa Tsaro a ZamfaraCOAS ya Nemi Karin Hadin Kan Sojoji da ECOWAS Kan Barazanar Ketare IyakokiSojoji Sun Kai Hari Sansanin Ƴan Ta'adda, Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Benue Yunwa da Tsananin Rayuwa Sun Sa Ƴan Tawaye 73 da Iyalansu Sun Mika Wuya — HQ TsaroDakarun Soji  Sun Ceto Sojan da Aka Sace a FilatoAn Tattara Bayanai Kan Hare-Haren Ta'addaci 367, An kashe Ƴan Ta'adda 52 a Watan SatumbaNajeriya @66: Gwamnatin Tarayya ta Karkata Kan Cigaba, Ayyukan Yi, da Inganta RayuwaNajeriya @66: Ministan Tsaro ya yi kira ga  Ƴan Najeriya da su Hada kai Domin Zaman Lafiya da TsaroPDP ta Zargi Gwamnatin Inuwa Yahaya da Shirya Katin Mambobi na Bogi Gabanin Zaben Fidda Gwani a Gombe
X whatsapp