Home Taska Ƙasurgumin ɗan bindiga, Turji ya ɗauki Alhakin Kashe Sojoji a Jihar Sokoto

Ƙasurgumin ɗan bindiga, Turji ya ɗauki Alhakin Kashe Sojoji a Jihar Sokoto

Ƙasurgumin ɗan bindiga, Turji ya ɗauki Alhakin Kashe Sojoji a Jihar Sokoto

Ƙasurgumin ɗan bindigar nan, Bello Turji, ya bayyana a wani sabon bidiyo, inda ya ɗauki alhakin kisan wasu dakarun sojoji a Jihar Sakkwato.

Lamarin ya faru ne bayan da sojoji suka tashi zuwa garin Bargaja da ke Ƙaramar Hukumar Isa, sakamakon harin ’yan bindiga suka kai da sanyin safiyar ranar Asabar.

Mazauna yankin sun ce ’yan bindiga sun kai farmakin ne tsakanin ƙarfe 12:30 na dare zuwa 3 na safe, inda suka riƙa harbe-harbe, lamarin da ya jefa jama’a cikin tsoro.

Yayin da sojoji ke kan hanyar zuwa wajen domin kai ɗauki, wani bam da aka dasa a kan hanya ya tarwatsa motarsu a hanyar Isa zuwa Bargaja.

Rahotanni sun ce aƙalla sojoji biyu ne sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata.

A cikin bidiyon da ya fitar bayan aukuwar harin, Turji, ya ce yana murna da mutuwar abokan gabansa.

Ya kuma yi iƙirarin cewa mutanensa sun samu nasara a kan jami’an tsaro tare da ƙwato dabbobin da aka ƙwace a wajensu.

Rahotanni kuma sun nuna cewa an shiga damuwa a yankin kan cewa Turji na ƙara samun ƙarfi da kuma samun sabbin makamai a yankin iyakar Sakkwato da Zamfara.

Wani mai rajin kare haƙƙin jama’a, Basharu Altine Guyawa Isa, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa Turji da wasu kwamandojinsa suna tara mayaƙa tare da horar da su.

Ya kuma ce wasu mayaƙa masu alaƙa da Boko Haram sun shiga cikin ƙungiyar domin taimakawa wajen horo da kuma kai hari.

Ya ƙara da cewa ƙungiyar ta samu makamai masu hatsari ciki har da na’urar gani cikin dare.

Hukumomi ba su tabbatar da waɗannan zarge-zarge ba, kuma ’yan sandan Jihar Sakkwato ba su mayar da martani ba lokacin da aka nemi jin ta bakinsu.

Waɗannan rahotanni na ƙara haifar da fargaba a tsakanin mazauna wasu yankuna na Jihar Sakkwato da kewaye.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Haba, Abba Bichi — Waɗannan Tallace-Tallacen Ranar Haihuwa Sun Wuce Iyaka! Daga Yushau A. ShuaibNAF ta Kaddamar da Aikin Ceto Bayan Jirgin Saman Soja ya Fado a OndoSojoji Sun Kashe Mayakin B'Haram, Sun Kama Wani a GeidamRijistar Masu Kaɗa Kuri'a a Najeriya ta Kai Miliyan 103 - INECMuna Kafa Sabbin Sansanonin Sojoji Domin Kare Al'ummomin da ke Cikin Hatsari – TinubuJirgin Sojojin Sama (NAF) ya Fado a Ondo Dauke da Mutane 32Sojojin Najeriya Sun Kaddamar da Sabbin Bataliyoyi 3 Don Karfafa Tsaro a ZamfaraCOAS ya Nemi Karin Hadin Kan Sojoji da ECOWAS Kan Barazanar Ketare IyakokiSojoji Sun Kai Hari Sansanin Ƴan Ta'adda, Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Benue Yunwa da Tsananin Rayuwa Sun Sa Ƴan Tawaye 73 da Iyalansu Sun Mika Wuya — HQ TsaroDakarun Soji  Sun Ceto Sojan da Aka Sace a FilatoAn Tattara Bayanai Kan Hare-Haren Ta'addaci 367, An kashe Ƴan Ta'adda 52 a Watan SatumbaNajeriya @66: Gwamnatin Tarayya ta Karkata Kan Cigaba, Ayyukan Yi, da Inganta RayuwaNajeriya @66: Ministan Tsaro ya yi kira ga  Ƴan Najeriya da su Hada kai Domin Zaman Lafiya da TsaroPDP ta Zargi Gwamnatin Inuwa Yahaya da Shirya Katin Mambobi na Bogi Gabanin Zaben Fidda Gwani a Gombe
X whatsapp