Daga: Usman Bello Balarabe, Kano. Fassara: Rabiu Sani Hassan
Bincike ya tabbata da Kamfanin ‘Yan Kwangilar da Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya sahalewa damar aikin Hanya a shekara 2019, babu wannan kamfani kwatakwata.
Ko da yake dai suma Jami’an Gwamnatin Jihar da aka tambaye su, sun kasa tantance zunzurutun kudi kimanin Naira Miliyan 110 da aka sahale domin samar da hanyar da ta lalace sakamakon rashin gyara.
Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano karkashin Dafta Abdullahi Umar Ganduje ta fara sahale aikin hanyar Ado Bayero dake Unguwar Dorayi Babba a Karamar Hukumar Gwale ne a shekarar 2019, kuma aka amince aikin zai ci Naira Miliyan 110 a cikin kasafin kudin shekarar 2019, 2020 da kuma shekarar 2021.
An amince da Naira Miliyan 38 domin gudanar da aikin a shekarar 2019, sannan sauran sahalewar ta biyo baya, sai dai Jaridar Economic Confidential ta bankado cewa anyi watsi da aikin, ba tare da nuna wata alamar za’a cigaba da yi ba.
Haka kuma jaridar ta Economic Confidential ta gano cewa kamfanin da aka sahalewa kwangilar na STONEGATE QUARIES LIMITED, bashi da rijista kwatakwata da hukuma, kuma duk kokarin da jaridar tayi ta kasa gano adreshin kamfanin.
Bisa la’akari da yadda kwararrun ma’aikatan awo tsawon hanya da kuma wasu cikin Al’ummar dake zaune a yankin sun tabbatar da titin nada nisan Kilomita guda (1).
*Babu Kamfanin*
STONEGATE QUARIES LTD, wanda ake ba da adreshin sa da gini mai lamba 1011 Domkat Bali Ln. Mabushi District, Abuja, shi ne Kamfanin gine-gine da aka ce ya sami kwangilar. Haka aka rubuta a jikin allon karfe dake dauke da cikakken bayani game da aikin, Dan kwangila da kuma wanda ke lura da aikin.
Dangane da bayanin da aka samu daga Hukumar dake Lura da yiwa Kamfanoni Rejista (CAC) ya bayyana cewa babu kamfanin cikin jadawalin kamfanonin da suka yi Rijista da ita, wannan ya nuna cewa kamfanin babu shi kwata kwata cikin kundin doka.
Sai dai duk kokarin Jaridar ta Economic Confidential na nemo sunan kamfanin a kafar yanar gizo, shafin Google bai nuna mata cewa akwai wannan kamfani ba.
Sai dai wani rahoto a hukumanci daga hukumar ta CAC ya bayyana a ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2022 yace akwai kamfanin gine gine wanda yayi kama da wannan amma sai dai adreshin su ya bambamta.
Kamfanin da gwamnatin Jihar Kano ta sahalewa Aikin sunan shi “STONEGATE QUARIES LTD” wanda ke da adreshin gini mai lamba 1011 Domkat Bali LN. Mabushi District, Abuja, amma shafin hukumar ta CAC akwai kamfani mai suna “STONEGATE ENGINEERING AND QUARIES LTD” wanda ke da adreshin gini mai lamba 5, Gana Unguwar, Maitama, Abuja,
*Mazauna Yankin Sun Kashe Sama da Naira Miliyan 14 Wajen Gyaran Hanyar*
Duk da Gwamnati ta amince ta naira miliyan 110 tun a shekarar 2019, al’ummar yankin sun yi karo karo inda suka hada kudi sama da Naira miliyan 14, suka kashe wajen gyaran titin domin su samu sukuni.
Read Also:
A wata ziyara da tawagar Economic Confidential tayi ta iske titin dauke da manyan ramukan da ruwa ke kwanciya, baya ga rashin ingantattun magudanan ruwa, duk da cewa tsaron shekaru 14 mazauna yankin na kokawa kan yadda hanyar ke cikin wannan yanayi, baya ga yanayin wahalar zirga zirga da suke fuskanta, sun koka kan yadda kanana da matsakaitan sana’oi ke fuskantar gagarumar matsala lokacin damuna saboda yanayin hanyar.
Shugaban Al’ummar yankin, Alhaji Usman Aliyu, wanda ke zaune a kan hanyar ta Ado bayero na tsahon shekaru 15, yace mazauna yankin sun bi dukkan hanyoyin da suka kamata wajen sanar da Gwamnatin halin da hanyar ke ciki ko ta dauki mataki amma hakarsu bai cimma ruwa ba.
“Tsawon shekaru 14 muna hada kudi a tsakanin mu domin gyaran wannan hanyar, mukan kashe a kalla Naira Miliyan 1 wajen gyara, wani lokacin mukanyi sau 1 wani lokacin sau 2 har sau 3 nuna yi domin gyaran hanyar a shekara, duk da kudin da Al’ummar wannan yanki suka hada.
“A shekarar 2019, Mun ga alamun yinkurin aikin hanyar ta Ado Bayero, inda aka ce gwamnatin Jihar Kano ta saki kudi saboda gyaran, inda aka jibge manyan motocin aiki na tsahon makwanni 2 kafin daga bisani a kwashe su” Kamar yadda yace.
Usman ya kara da cewa hanyar ta Ado Bayero, hanya ce da ta dake sada al’ummar yankin da makarantu, da kuma babban masallaci, Dan Sarari, ga kuma yadda mazauna yankin dake fama da cututtukan dake da nasaba da huhu ke shan wahala, sakamakon shakar kura mai sakamakon watsin da akayi da aikin.
*Yadda Masu Kananan Sana’oi Ke Fuskantar Matsala*
Kananan ‘Yan kasuwa dake gudanar da harkokin kasuwanci akan titin na Ado Bayero sun shaidawa Jaridar Economic Confidential yadda rashin kyauwun hanyar ke shafar harkokin kasuwancin su sakamakon rashin ingancin hanyar baya ga biyan makudan kudin sufurin kayayyakin.
Wani Dan Kasuwa mai suna Ambasada Abdulyasar Aminu yace watsi da aikin titin ba kawai yana kawo cikas ga ci gaban kasuwancin al’ummar yankin ba ne kadai, yana shafar ci gaban tattalin Arziki da dorewar sa a Jihar Kano.
“In takaici maka bayani ko da a shekara data gabata wakilin kafar BBC ya ziyarci yankin don yin rahoto game da ambaliyar da muke fuskanta duk lokacin damuna, abinda baya rasa nasaba da watsi da wannan aikin hanya da kuma rashin magudanar ruwa a hanyar.
“Muna kira ga gwamnati da ta yi abinda ya kamata saboda yadda gidajen mu ke fama da ambaliyar ruwa a lokacin damuna, yayin da muke fama da karancin abokan hulda kasuwanci sakamakon kurar da ke shiga Shaguna, Rumfuna da Gidajen mazauna wannan yanki.
Wani Dan Kasuwa dake kasuwanci a yankin, Mahdi Bashir ya bayyana cewa akwai fargabar Al’ummar wannan yanki ka iya tashi su koma wata unguwar sakamakon watsi da hanyar da aka yi.
Bashir ya kara da cewa “Lokacin damuna yanayin yafi kazanta ga dukkan ‘Yan kasuwa da mazauna yankin, ta yadda suke shan wahala tare da gwagwarmayar killace gidajen su daga ambaliyar ruwa, lokacin rani kuwa kurar dake tasowa daga titin ita ce babbar matsalar da Al’ummar yankin ke fuskanta.
*Yadda Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano ya Kalubalanci Dan Jarida: “Mene ya shafe ka da aikin hanyar?”*
A kokarin samar da da daidaito ta hanyar jin ta bakin ko wanne bangare kamar yadda Aikin Jarida yayi tanadi, Economic Confidential ta tuntubi kwamishinan ayyuka na Jihar Kano Engr. Idris Wada Saleh, bayan kiran wayar tarho da sakon karta kwana da aka yi masa, daga karshe ya nemi wakilinmu da ya bayyana masa shin aikin hanyar na mazaba ne ko Jiha ko kuma gwamnatin tarayya, ko kuma aikin wani mutum guda ne.
Bayan da wakilin namu yayi masa cikakken bayani kan aikin, sai ya kada baki yace “Waye ya ce maka bai cancanta ba?, kuma menene matsalarka da hakan? Ba a yi aikin yadda ya kamata ba ko kuma bai biya harajin sa ba?.”
Daga: Economic Confidential
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 6 minutes 55 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 12 hours 48 minutes 20 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com