Ministan Sufuri Rotimi Amaechi yace an dakatar da Hukumar Lura da Sufurin Jiragen Kasa ta Nijeriya (NRC) daga sayar da tikitin hawa Jirgin ga matafiya.
Ya bayyanna hakan ne yayin da yake gabatar da takardar sahelewar saida tikitin da za’a sayar ta yanar gizo (E-ticketing) na Legas zuwa Ibadan dana Itakpe zuwa Warri ga hukumar ICRC
Ameachi Yace an dauki wannan mataki ne domin dakile cin hanci da rashawa da kuma barazanar rashin tsaro da Hukumar ta NRC ke fuskanta.
Ya kara da cewa tun bayan kaddamar da wannan tsari na E-Ticketing kudin shigar da ake samu ya rubanya.
Read Also:
PRNigeria ta rawaito Ameachi na cewa daukar wannan mataki ya zama waji ne kasancewar yadda matsalar rashin tsaro ke kara addabar hanyoyi a Nijeriya
“Duk da dai baza mu iya magance matsalar rashin tsaron da cin hanci da rashawa dari bisa dari ba, amma hakan zai rage matsalar rashin tsaron da muke fuskanta”
“yanzu gwamnatin Tarayya taga Alfanun wannan tsari, ta hanyar kara samun kudin shiga daga miliyan dari daya duk wata zuwa miliyan dari 4.”
Idan za’a iya tunawa PRNigeria ta rawaito cewa wasu ‘Yan Bindiga sun dasa abun fashewa a kan titin jirgin kasa daga Abuja zuwa kaduna Abinda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da batan wasu.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 35 minutes 28 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 16 minutes 54 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com