Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutum 595 daga cikin mutum 21,877 da suka kamu da cutar Kwalara a Jihar cikin shekarar 2021.
Babban Sakataren Hukumar ta Lafiya Salisu Mu’azu ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar talata a Jihar.
“Barkewar cutar kwalarar na da alaka dari bisa dari da tsaftar Muhalli ko kuma yadda al’umma ke gudanar da muhallin nasu, abin mamaki ne ace yadda gwamnatin Jihar ta sami nasarar samar da ingantaccen ruwan sha, amma cutar ta ta yi sanadiyyar mutuwar mutane masu tarin yawa.”
Yace don kawo karshen yawon mace-macen da aka samu sakamakon cutar a shekarar data gabata, ma’aikatarsa ta samar da daukin gaggawa, a shekarar 2022.
A cewarsa “muna da tawagar dake aiki nan take, amma lokacin damuna tawagar kan mayar da hankalin ta wajen yin rigakafi, da kuma wayar da kan al’umma da sauran masu ruwa da tsaki dangane da sake barkewar cutar.
Read Also:
Mu’azu ya kara da cewa a shekarar 2021 gwamantin jihar ta sami nasarar yin riga kafin ga mutum 946,325 da kuma 904,169 a kananan hukumomin Birnin Kudu, Dutse da kuma Hadejia don magance cutar.
“sannan kuma an sami nasarar yin riga kafin ga kananan yara da basu gaza shekaru 5 ba kimanani 1,720,742 da 1,782,026 a watan Yuni da Julin shekarar 2021.
Idan dai za’a iiya tunawa a ranar 21 ga Nuwamban 2021 Hukumar Kare Yaduwar Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa ta bayyana cewa ana sami mutum 3,566 da mutum 103,589 da ake zargin sun kamu da cutar ta kwalara a jihohi 32 na Nijeriya ciki har da birnin tarayya Abuja.
Hukumar tace kashi 3.4 na wadanda suka kamu da cutar sun fito ne daga jihohi 4 da suka hadar da jihar Bauchi (19,470), Jigawa (13,293) Jihar Kano (12,116) sai kuma Jihar Zamfara (11,918) wanda yake matsayin jumullar kashi 55 cikin dari.
A kokarin da jihar ke yi na shawo kan barkewar cutar a shekarar 2021, jihar ta samu gagarumar nasara ta hanyar jigilara mata masu juna biyu, dake shan wuyar isa asibitoci don karbar kulawa.
Mu’azu yace Jihar ta Jigawa bata sami ko da mace guda data rasa ranta sakamakon cutar ba, ya kara da cewar ma’akatar ta kashe sama da Naira Miliyan 8.7 kan Shirin kawar da cutar tare da daukar direbobi 600 a shekarar 2021
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 29 minutes 7 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 10 minutes 32 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com