Bankada: Yadda Gwamnan Jihar Gombe ke Haramtawa ‘Yan Jarida Fadin Albarkacin Baka

Daga: Abdulsalam Mahmud,          Fassara: Rabiu Sani Hassan

Hankula na cigaba ta tashi, fargaba na kara shiga zukatan Al’ummar Jihar Gombe, sakamakon Yunkurin Gwamnan Jihar Muhammad Inuwa Yahaya na dakile kafafen yada labarai da fadin albakacin baka.

A kalla ‘Yan Jarida 3 ne aka kama ko kuma aka tursasasu gami da tsoratar da su Kan wasu tuhume tuhume da ake musu na bata suna, bayan sun wallafa wani labarin binciken na gaskiya.

Haka kuma Jarida PRNigeria ta bankado cewa yanzu haka Gwamna Yahaya na bin diddigin wasu ‘Yan Jarida da suka gudanar da binciken.

Ga misali gwamnan ya haramtawa mawallafin Jaridar Daylight, Dahiru Hassan Kera shiga Jihar Gombe, kuma muddin ya shiga za’a kamashi wato dai ‘persona non grata’ kuma tuni ya fice daga cikin jihar.

Ta cikin wata ganawa da Dan uwa ga Kera, ya shaidawa PRNigeria cewa dan uwan nasa bai taka kafarsa cikin jihar ba tsawon watanni da yawa, inda ya shiga boye boye bayan Gwamna Yahaya ya yi barazanar yin maganin sa ta hanyar daukar kwakkwaran mataki a kansa.

An dai fara daukar wannan mataki ne mai kama da Zalunci kan Dan Jaridan tun bayan da ya wallafa wani labari a jaridar da ake wallafawa a yanar gizo, dake bayyana yadda rudani kan dumbin basussukan da ake bin Jihar Gombe a karkashin Gwamnatin Inuwa Yahaya.

Sauran kafafen yada labarai irin su The Peoples Gazette, Premium Times da Sahara Reporters, duk sun wallafa kalaman kungiyoyi daban-daban, inda suka yi Allah wadai kan batun bashin.

Ta cikin wata ganawa da PRNigeria tayi da Kera ta wayar tarho, ya bayyana kudurin na Gwamnan matsayin bita da kulli irin na siyasa, kasancewar ya kasa daukar mataki kan sauran jaridun da suka wallafa labari makamancin nasa.

“baya ga labarin dinbin basussukan da jaridar ta wallafa, Gwamna Yahaya bai gamsu da shawarar dana yanke na tsayawa takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Gombe ba, a zaben shekara mai zuwa,” inji shi.

A cewar Kera, tsoffin gwamnoni biyu da wasu fitattun ‘yan siyasa biyar a jihar Gombe da suaran sannan Nijeriya suka yi yunkurin shiga Tsakani domin daidaita lamarin, amma gwamna Yahaya ya tsaya kyam akan bakar sa.

“Saboda Gwamnan na kasa ziyartar kanena da aka kwantar a Asibitin Gombe lokacin da yake fama da rashin lafiya, kafin rasuwar sa a ranar 21 ga watan Aprilun, 2022.

“ba wanne kadai matsalar ba, ban sami damar halartar jana’idar sa ba, domin ban san irin tarkon da Gwamna Yahaya ya dana min ba idan na shiga Jihar ta Gombe ba.

Baya ga wannan mawallafi, akwai wani dan jarida a jihar da ya samu tsangwama fiye da Kera, a hannun Gwamna Yahaya, shine wakilin Muryar Amurka dake aiki a jihar ta Gombe.

A takaice dai, ta cikin wata murya da aka nada ta wayar tarho tsakanin Gwamnan da wakilin na Muryar Amurka, wanda PRNigeri ta samu, ta cikin wasu kalamai da Gwamna Yahaya yayi a fusace yana mai bayyana cewa zaiyi maganin wakilin na Muryar Amurka, bisa wani labari da yayi wanda bai yiwa gwamnan dadi ba.

Da yake Karin haske kan lamarin, wakilin na murya Abdulwahab Muhammad, da ake Magana akan say ace barazanar gwamnan bata razana shi ba.

Ya bayyanawa PRNigeria cewa “A cikin kwanaki 100 na farko da Gwamna Yahaya yay ikan Mulki, na yi hira da shi, na kuma yi masa tamabaya kan matakin da ya dauka na korar matasa sama da 4,000 wanda Gwamna Alh. Ibrahim Hassan Dankwambo, ya dauka aiki a cibiyar tsaro ta sirri ta jihar Gombe.

“Amma yayin da yake bada amsa kan tambayar, sai ya kada baki yace “ai wadanda aka dauka aikin sun an dauke su ne domin su taimaka wajen ciyar da siyasar tsohon Gwamna Dankwambo gabanin zaben shekarar 2019. A cewarsa, wadanda aka dauka zasu iya shiga aikin dan sanda ko soja idan suna da sha’awar aikin damara.

“Don haka, wajen daidaita labarina wato (balancing), na kuma sami zarafin tattaunawa da kakakin jam’iyyar PDP na Jihar Gombe, wanda ba kawai ya kalubalanci matakin gwamnan bane, ya ayyana kwanaki 100 da gwamnan yayi akan karagar gwamnatin Jihar matsayin ‘Bakar Rana’ ga Jihar, babu dadewa labarin ya fito nan Gwamnan ya kirani a waya ta inda ya shiga bata nan yake fita ba, yana fadar maganganu marasa dadi.

Ta cikin wata tattaunawa da wakilin PRNigeria ta wayar tarho wani mai tasiri a kafafen sada zumunta na zamani, Sani Labaran ya bayyana mummunan zaluncin da shima ya fuskanta a hannun ‘yan daba da Direban Gwamna Yahaya, a watan satumban da ya gabata.

A cewar Sani labaran yace cin zarafin da ya fuskanta a hannun  wasu ‘yan daba da ake zargin suna yiwa Gwamna Yahaya aiki, baya rasa nasaba da yadda ya yi wasu rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta ba, yana sukar wasu manufofin Gwamnan jihar ta Gombe ba.

Labaran, yace a karshen watan satumban shekarar data gabata ina tsaye a wani garejin mota domin gyara motata, nan wasu mutum 3 cikin wata mota kirar Jeep dake dauke da lambar gwamnatin jihar Gombe suka yiwa garejin tsinke

“Nan suka hau kaina da mari, mangari gani da bugu da sanduna wasu kuma dauke da wasu makamai inda suka ji min muggan raunika a sassan jikina gani da kai na.

“daga bisani aka tsare ni bisa umarnin gwamnatin Jihar na tsawon kwanaki 11, daga bisani kuma na shaki iskar ‘Yanci, bayan zalunci da muguwar azabar da na dandana a ofishin ‘Yan Sanda lokacin da ake tsare da ni, ya sa ko tafiya bana iya yi gami da yin fitsari cikin sauki, wanda hakan ya sanya sai da aka yi min tiyata bayan an sake ni.

Sai dai dukkan kokarin da PRNigeria tayi ta samin damar ganawa da guda cikin manayan jami’an Gwamnatin jihar ta Gombe hakarta bai cimma ruwa ba.

Haka zalika babban daraktan yada labarai na Gwamnatin jihar Gombe, bai amsa kiran da wakilin PRNigeria ya yi masa ta wayar tarho ba. Har ila yau bai mayar da martini ga sakon whatsapp da aka tura masa ba,

 

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 14 hours 42 minutes 9 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 23 minutes 34 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com