Majalisar Wakilan Nijeriya ta Bukaci Karin Girke Karin Jami’an Tsaro a Jihar Taraba

Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci Hafsan Sojin kasar da Babban Sifeto Janar su kara girke dakaru a jihar Taraba.

Da yake Karin haske kan kisan da ‘Yan bindiga suka yi a jihar yayin da yake gabatar da kudirin a zaman majalisar na ranar 10 ga watan Mayu, Dan Majalisa daga Jihar Taraba Usman Danjuma yace ‘Yan Bindiga yayin wani hari da ‘Yan Bindigar suka kai tsakar dare sun halaka Al’ummar kauyen da dama.

Mafi yawan Mazauna Kauyen na Tati dai manoma ne, sai dai harin na ‘yan bindiga ya tarwatsasu.

“sakamakon kiraye-kiraye neman dauki da mazauna kauyen suka yi, jami’an tsaro sun yi tattaki zuwa yankin inda ‘yan ta’addan suka yi musu kwantan bauna, inda suka halaka sojoji da shida.

Wannan dai na zuwa ne bayan da ‘yan bindiga suka halaka wani jami’in Dan sanda da wani farar hula a shingen ababen hawa, inda kwamanda bataliya ta 93 yayi batan dabo yayin gudanar da atisayen kawar da ‘Yan Ta’addan.

“an kai korafe-korafe ga jami’an tsaro kan yadda ‘yan bindigar ke zirga-zirga a kauyen a makonnin da suka gabata.

“ wannan ce ta sanya jami’an tsaron Musamman bataliya ta 93 da wasu Karin dakarun hadin gwuiwa, suka farwa ‘yan Ta’addan tare da samun nasarar kwace muggan makamai a hannun su.”

Dan majalisar ya nuna damuwar sa matuka kan yadda ‘yan bindigar ke sake kwarara yankunan Nijeriyar.

Yayin da majalisar ke amincewa da kudirin ta yi kira ga Hukumar Bada Agaji Gaggawata NEMA ta gaggauta kai Agaji ga Al’ummar da abin ya shafa a karamar hukumar Takum ta jihar Taraba.

Da yake ganawa da manema labarai, Danjuma yace ‘yan bindiga sun fito ne daga jihar Borno da jihar Plateau.

“Muna fuskantar babban kalubalen tsaro daga ‘yan bindiga a kudancin jihar Taraba, an kashe sama da mutane 42 cikin kwanaki 3 da suka gabata tare da kone gidaje 6 a karamar hukumar takum, kuma muna zargin ‘yan bindigar sun fito ne daga jihohin Filato da Borno.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 15 minutes 8 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 10 hours 56 minutes 33 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com