Rundunar ‘Yan sandan kasa da kasa ta INTERPOL dake yaki da masu damfarar yanar gizo a yankin Asiya tabi diddigin wasu mutun 3 da ake zargi da gudanar da damfara a Nijeriya.
Hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta EFCC, ta cafke wadanda ake zargin ne a wani samame da ta kai unguwar Ajegunle dake Legas a kudu maso yammacin Nijeriya, da kuma Benin dake kudu masu kudancin kasar.
Wannan dai na kunshe ne ta cikin wata takardar sanarwa da aka raba ga manema labarai mai dauke da sa hannun kakakin hukumar ta EFCC Welson Uwujaren, mai kwanan watan 31 ga watan Mayun 2022.
Read Also:
Sumamen na cikin wani bangare na yaki da masu ta’adar ta damfara a kafar yanar gizo a fadin duniya mai lakabin “killer Bee” wanda ta hadar da jami’an ‘yan sandan kasa da kasa na INTERPOL, National Central Bureau (NBCs) da Jami’an tsaro na kasashe 11 na kudu maso gabashin Asiya.
Haka kuma ya biyo bayan wani rahoto da aka wallafa dake cewa, wasu ‘Yan Nijeriyar na gudanar da harkokin damfarar a kasar wadanda ke aiki daga gabar tekun yammacin Afirka, inda suke amfani da wata muguwar cutar Na’ura ta Remote Access Trojan (RAT) da aka fi sani da Agent Tesla.
Mutanen su 3 da jami’an suka sami nasarar kamewa nada kimanin shekaru 31 zuwa 38, an kama ko wannen su da takardun bogi da suke amfani dasu wajen gudanar da ayyukan damfara.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 23 minutes 56 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 5 minutes 21 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com