Kasar Rasha Na Shirin Korar Hazikin Dalibin Likitan ‘Dan Najeriya ‘Kan Cin Hanci Da Rashawa A jihar Sokoto

Kasar Rasha na Shirin korar Dalibin likitanci Dan Nijeriya mai kwazo sakamakon cin hanci da rashawa a hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Sokoto.

PRNigeria ta samu labarin cewa wani dalibi dan Nijeriya dake shekarar karshe a jami’ar jihar Irkutsk (ISMU), wato Usman Yahaya, hukumomi a jami’ar na Shirin tiso kiyarsa daga kasar Rasha zuwa Nijeriya daga yanzu zuwa ko wanne lokaci.

Yahaya haifaffen jihar Sokoto a arewacin Nijeriya dalibin likitanci, ya shafe sama da wata guda yana tsare a kasar ta Rasha.

Idan za’a iya tunawa a makon daya gabata PRNigeria ta rawaito cewa Yahaya ya sami nasarar lashe lambar yabo ta dalibin likitanci daya fi ko wanne dalibi a Nahiyar Afirka wato Best African Medical Student a cibiyar kimiyya ta Rasha.

Jami’ar likitancin ta fara dakatar da dalibin ne a lokacin da Gwamnatin Jihar Sokoto ta kasa biyan kudin tallafin karatun sa da ya kare.

Daga bisani hukumomin shige da fice na Turai suka tsare shi a sansanin shige da fice na Rasha da ke Angarsk Irkutsk, sakamakon dambarwar cin hanci da rashawa data dabaibaye Hukumar Bada Tallafin Karatu a jihar sa ta Sokoto.

Ana zargin Daraktan dake lura da daliban dake karatu a kasashen waje na hukumar ba da tallafin karatu ta jihar Sokoto, Kabiru Labaran, wanda ya sha kwana da wasu makudan kudade daga cikin kudaden tallafin karatun Yahaya da Gwamantin Jihar Sokoto ta amince da su duk shekara tun daga shekarar 2016.

Yahaya ya bayyana sau 2 a gaban wata kotun kasar Rasha, kuma idan aka same shi da laifi za’a iya korar shi daga jami’ar ta ISMU, tare da tsare shi ko kuma a haramta masa shiga kasar Rasha a nan gaba.

PRNigeria ta sami labarin cewa a safiyar ranar Alhamis (2 ga watan Yuni, 2022) wasu cikin Ma’aikatan jami’ar ta IMSU da wani Jami’in ‘Dan sandan kasar sun tisa kiyarsa zuwa Ofishin Kula da shige da fice na kasar Rasha Domin sanya hannu a kan takarda zargi.

Ta cikin wata tattaunawa da PRNigeri tayi da shugaban kungiyar Daliban Nijeriya dake karatu a kasashen Turai Bashiru Muhammad, yayi kira ga Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal daya sa baki kan halin da Yahaya yake ciki.

Muhammad wanda dalibi ne a Jami’ar Conventry ya bayyana damuwar sa matuka, kan yadda Gwamnan jihar ta Sokoto Aminu Tambuwal yake kula da daliban jihar Sokoto dake kasashen waje muddin ba’a dauki matakin ceto Yahaya cikin gaggawa ba.

Shugaban kungiyar ta ANSE yace ya tuntubi masu ruwa da tsaki a Jami’ar da kuma Gwamnatin jihar Sokoto domin nemo bakin zaren matsalar.

A halin da ake ciki dai shugaban kungiyar dake yaki da cin hanci da rashawa ta transparency International Malam Auwal Musa Rafsanjani, ya bukaci a binciki jami’an dake da hannu a badakalar data ta sanya Yahaya cikin tashin hankali a hukumar.

Rafsanjani wanda kuma shi ne Babban Darakta na Cibiyar Bayar da Shawara ta Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC), ya roki Gwamna Tambuwal da ya sa baki kan halin da dalibin ke ciki.

Ya kuma bukaci hukumomin Yaki da Cin Hanci da Rashawa su binciki zargin karbar rashawa da ake wa Hukumar Tallafin Karatun ta jihar Sokoto.

“Wannan abin takaicine matuka yadda hazikin dalibin da ke ajin karshe na kammala karatun likitanci a Babbar Jami’ar Kiwon Lafiya a kasar Rasha kuma dan asalin jihar Sokoto ke fuskantar wannan mawuyacin hali yayin da muka san yadda manyan mu ke daraja ilimin ‘ya’yansu a makarantu mafi tsada a kasashen waje.

“Don haka muna kira ga Gwamna Tambuwal na Sokoto, jihar dake da karancin kwararrun likitoci, daya sanya baki a game da halin da wannan Dalibi talaka ke ciki, muna kuma kira ga hukumar EFCC da ICPC da su binciki ayyukan rashawar da ake yi a hukumar ba da tallafin karatu ta jihar Sokoto,” inji Rafsanjani.

Ko da aka tuntubi kwamishinan Yada Labarai na Jihar Sokoto Malam Isa Galadanci ya shaidawa PRNigeria cewa Yahaya da kansa ya nemi a dauke shi daga Jami’ar Sudan dake birnin Khartoum zuwa kasar Rasha a shekara 2014 ba tare da sanin hukumar bayar da tallafin karatun ba.

Sai dai ya ce: “Gwamna yana Abuja yanzu, amma ina tabbatar muku cewa, za mu gana da shi a duk lokacin da ya dawo, kuma mu roke shi da ya sa baki cikin lamarin Yahaya, bisa dalilin jin kai”

By PRNigeria

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 15 hours 24 minutes 46 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 17 hours 6 minutes 11 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com