Dakarun sojin Operation Delta Safe sun sami nasara tarwatsa matatun Mai guda 40 dake gudanar da aikin tace mai ba bisa ka’ida ba a jihar Delta dake kudancin Nijeriya.
Daraktan yada labaran rundunar sojin kasar Manjo Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi na mako-mako kan yunkurin dakarun sojin kasar na kawar da dukkan wasu ayyukan ta’addanci da muggan dabi’u.
Onyeuko ya kara da cewa kimanin litar danyen Mai 1,107,400 da kuma litar AGO 456,450 sojojin Nijeriyar suka sami nasarar kwatowa a yayi atisayen.
Yace “a cikin dan kankanin lokaci sojojin sun bankado tare da lalata matatun mai guda 40 dake aiki ba bisa ka’ida ba, da kuma tankunan ajiyar main a karfe guda 165 sai kuma wasu ramukan ajiyar mai guda 23 da jirgin ruwa na katako guda 5 dake dauke da man.
Read Also:
“Dukkan abubuwan da aka kwato da kuma masu aikata laifi da aka kama an mika su ga hukomomin dake suka dace domin cigaba da daukar mataki”
Haka zalika Oyeuko, ya bayyana cewa dakarun da ke aiki a karkashin rundunar OCTOPUS Grip na kara matsa lamba kan masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da sauran masu aikata laifuka, wanda hakan ya kassara barayin mai a kasar.
“Operation OCTOPUS GRIP hadin Gwuiwa da dakarun DELTA SAFE sun gudanar da wasu atisaye a wasu rafukan, garuruwa da suka hadar da Jesse, hanyar Warri dake karamar hukuma Eithiope ta yamma, Banga, Mondongho Rafi a karamar hukumar Warri ta Kudu Maso Yammacin Jihar Delta da dai sauran yankuna.
Ya kara da cewa “Sauran wuraren sun hadar da rafin Okubotowa dake karamar hukumar Akassa Brass, Ikebiri ta kuduncin karamar hukumar Ijaw ta jihar Bayelsa akwai yankunan Gwathrone da ke karamar hukumar Bonny ta Jihar Rivers, da karamar hukuma Akpabiyo a Jihar Cross River da kuma Effiate Waterway Ibaka a jihar Akwa Ibom”.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 18 hours 7 minutes 57 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 49 minutes 22 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com