Wasu ‘yan bindiga sun harbe a kalla mutum 6 a unguwar Sabo dake garin Ondo, a jihar Ondo a daren laraba.
Wannan dai na zuwa ne sa’oi 72 bayan wani harin ta’addanci da aka kai kan mujami’ar St. Francis catholic Church, a garin Owo inda suka halaka mutum 40, yayin da mutune da dama suka sami muggan raunuka.
Read Also:
An ruwaito cewa maharan saman Babura suka kai harin, duk da cewa wata majiya ta bayyanawa PRNigeria cewa sai da suka yiwa wasu mazauna yankin fashi kafin su tafi.
Kakakin rundnar ‘yan sandan Jihar Uwar gida Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da faruwar lamarin, said ai tace ayyukan fashi ne da makami ba ‘yan bindiga, amma tuni jami’an hukumar suka bi sahu domin daukar matakan da suka dace.