Farfesa Gwarzo Ya Tallafawa Dalibin Nijeriya A Rasha Da Naira MIliya Daya

Wanda ya assasa Jami’ar Maryam Abacha wato Maryam Abacha American University (MAAUN) Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bada tallafi naira miliyan 1 ga hazikin dalibin likitanci Usman Yahya, wanda ke tsare a hannun hukumar Shige da ficcen kasar Rasha.

Makwanin 2 da suka gabata Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa Yahaya wanda ya cibiyar Nazarin Kimiyya ta kasar Rasha ta karrama da lambar yabo matsayin Dalibin Likitanci mafi hazaka, a Jami’ar Jihar Irkutsk (ISMU), hukumar makarantar ta fara dakatar dashi daga shiga dakin kwanan Dalibai a harabar Jami’ar, sakamakon kin biyan masa kudin makaranta da gwamnatin jihar Sokoto tayi.

Tallafin zunzuruntun kudin da Farfesa Gwarzo ya bayar, wanda kungiyar Daliban Nijeriya a kasashen Turai ta karbar, ya biyo ta hannun Manajan Jaridar PRNigeria dake jihar Kano, Adnan Mukhtar.

A cewar Gwarzo, akwai bukatar ‘yan Nijeriya masu kishin kasar da su gaggauta kai dauki ga Yahaya, don tabbatar da ganin ya cimma burinsa na rayuwa daya sanya a gaba.

“Makomar Usman Yahaya tana cikin hadari, dole ne mu yi wani abu don tabbatar da cewa ya cigaba da karatun sa, tare da karbo shi daga hannun hukumomin kasar Rasha, haka zalika wannan kudi naira miliyan 1 dana bayar ta hannun kungiyar ANSE zata taimaka, kuma muna sa rana akwai gudunmawa daga wajen masu hannu da shuni na Nijeriya wadda zata taimaka wajen cire Yahaya daga halin da yake cike a halin yanzu.

Da yake bayani dangane da wannan tallafi da Farfesa Gwarzo ya bayar, shugaban kungiyar Daliban ta ANSE, ya sake yin kira ga gwamnatin jihar Sokoto da ta yi Adalci gami da jinkan ga Yahaya, tare da gaggauta taimakawa wajen magance matsalolin da yake ciki a kasar ta Rasha.

“Ba mu da bakin da zamu godewa Farfesa Gwarzo, domin ya taimaka matuka a kokarin da muke na ceto Usman Yahaya, don haka muna fata sauran Attajirai da masu hannun da Shuni su yi koyi da shi,” Inji Shi.

Usman Yahaya dai ya shiga cikin halin kakanakayin ne bayan da hukumar Jami’ar ta kore shi daga cikin harabarta, sakamakon wasu ayyukan cin hanci da Rashawa a hukumar bada tallafin karatu ta jihar Sokoto, da ake zargi ya haifar da jan kafa a wajen biya masa kudin karatu, hukumomin shige da fice sun tsare shi a sansani sun a Angarsk Irkutsk.

An dai zargi wani jami’in hukumar ba da tallafin karatu ta jihar Sokoto ne ke da hannu a wannan ta’asa, wanda ya kwashe makudan kudaden daga cikin kudaden tallafin karatu na daliban kasashen waje da Gwamnatin jihar Sokoto ta amince a fitar duk shekara, tun daga shekarar 2016.

Yahaya ya bayyana sau 2 a gaban wata kotun kasar Rasha, kuma idan aka same shi da laifi za’a iya korar shi daga Jami’ar ta ISMU, tare da tsare shi, koma a haramta masa shiga kasar ta Rasha.

Ko da PRNigeria ta tuntubi sashen hulda da dalibai na Jami’ar, Ms Elena Orel tace hukumar Jami’ar bata tsare dalibin da karfi ba karfi ba domin ta wulakan ta shi.

Tace kawai an kori Yahaya daga wajen zaman dalibai ne sakamakon karya dokokin shige da fice na kasar, wato rashin cikakkun takardu.

“An kai shi sansanin shige da fice domin samun damar gyara bisa ko sabuntata, babu wani nau’i na wulakanci ko cin zarafi daga hukumar, dalibin yana da damar gudanar da al’amurra  sa cikin ‘yanci.

“Duk da haka, bayan samun wasika daga masu daukar nauyinsa daga jihar Sokoto a Nijeriya, a halin yanzu dalibin yana can a masaukin jami’ar domin kare lafiyar sa.

“amma idan a karshe dalibin ya kasa sabunta takardunsa, babu shakka ana iya fitar da shi daga masaukin daliban.

 

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 14 hours 56 minutes 10 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 37 minutes 35 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com