Home Labarai Dan Bindiga 1 Ya Mutu ‘Yan Sanda Sun Kama 3 A Jihar...

Dan Bindiga 1 Ya Mutu ‘Yan Sanda Sun Kama 3 A Jihar Benue

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Benue sun sami nasarar kame wasu da ake zargin na da hannu a kai harin garin Igama na karamar hukuma Okpokwu dake jihar.

ta cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jihar Catherine Anene ya fita a ranar Alhamis, yace wadanda ake zargin dai ya mutu ne sakamakon raunin harbi da ya samu a gwamzawar da jami’an ‘yan sandada gugun ‘yan bindigar.

Wakilin mu ya rawaito mana cewa maharan sun afka garin a yammacin ranar lahadi inda suka halaka mutum 15, daga bisani suka banka wuta a gidajen Al’ummar garin.

Ta cikin sanarwa rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da jibge jami’anta hadin gwuiwa da sauran jami’an tsaro, domin bincika lungu da sako na dazukan dake yankin.

“A ranar 15 ga watan Yuni, misalin karfe 5 na safe, maharan dake makale a cikin daji, sun yi artabu da ‘yan sanda wanda ya kai ga an cafke Umar Nuhu, Dauda Alhaji, Musa Dako da Umaru Alhaji Sale.

“Daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Musa Dako ya samu raunuka kuma an kwantar da shi a Asibitin St. Mary’s dake Okpoga inda a karshe ya mutu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp