Train attack: Reps ask Buhari to secure release of remaining 51 kidnapped victims
Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari daya gaggauta daukar matakin ganin an sako sauran fasinjoji 51 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a a wani yarin jirgin kasan Abuja zuwa Kano.
Har ila yau, majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti mai karfi don ganin an kubutar da wadanda ke hannun ‘yan bindigar, dadukkan wadanda ke hannun ‘yan bindigar a fadin kasar, gami da bayar da taimako ga iyalan wadanda aka yi garkuwa da su.
Wanna bukata ta majalisar ta biyo bayan Nazari kan wani kudiri da Bamidele Salam da wasu ‘yan majalisar su 10 suka gabatar a zauren majalisar.
Read Also:
PRnigeria ta rawaito Dan majalisar Salam Ya gudanar da wani tattaki shi kadai a kwaryar birnin tarayya, wanda ya bukaci a sako wadanda akayi garkuwa dasu.
Cikin kudirin, dan majalisar ya bayyana cewa sashe na 14 (2) (b) na kundin tsarin mulkin da aka yiwa kwaskwarima 1999, ya bayyana cewa, tsaro da jin dadin jama’a shi ne babbar manufar gwamnati, kamar yadda sashe na 17 (2) (b) na kundin tsarin mulkin kasar ya bayyana muhimmancin dan Adam tare da inganta martabar sa da kare ta.
Ya kara da cewa, tsawon shekaru 10 da suka wuce, ta’addanci, ‘yan fashi masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, gami da munana laifuka sun zamo annoba ga tsaron kasar a sassa daban-daban na kasar.
Da take amincewada kudirin, majalisar wakilan ta umarci dukkanin kwamitocin da abin ya shafa na majalisar da su tabbatar da aiki da kudirin.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 10 hours 44 minutes 35 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 12 hours 26 minutes 0 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com