Dakarun Sojin Nijeriya Sun Sake Tarwatsa Maboyar IPOB/ESN

Dakarun sojin Nijeriya sun sake samun nasarar tarwatsa maboyar mayakan haramtacciyar kungiyar ‘Yan Awaren Biyafara ta IPON ko ESN a jihohin Anambra da Enugu dake kudancin kasar.

Wannan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labaran rundunar sojin Birgediya Janar Oyema Nwachukwu mai dauke da kwanan watan 26 Yunin 2022, wadda aka raba ga manema labarai.

Sanarwar tace dakarun hadin gwuiwar da suka kai 302 sun kunshi sojin kasa dana ruwa, jami’an tsaro na farin kaya DSS jami’an rundunar ‘yan sandan Nijeriya, sun sami nasarar tarwatsa maboyar dake matsayin mallakin mayakan na IPOB ko kuma ESN a kauyukan Idara Nnebo da Ihe Mbosi gami da Ukpor duk a karamar hukumar Nnewi ta kudu dake jihar Anambra.

A wani aikin share fage da aka gudanar da sanyin safiyar Asabar 25 ga watan Yuni 2022, sojoji sun fatattaki ‘yan kungiyar IPOB da ke gudanar da ayyukan ta’addanci a maboyar su ta hanyar yin amfani da wasu makamai da kuma gogewar aiki.

a yayin gudanar da atisayen, dakarun sojin sun sami nasarar kwato bindigu kirar AK47 guda 2 da kwanson shirya Alburusai makare, sai kuma Alburusai na musamman masu tsayin mita 7.62 da dai sauran manyan makamai, sauran kayan da suka kwato sun hadar da injin bada hasken wutar lantarki na (Generator).

A wani atisayen makamancin wannan dakarun sojin dake bataliya ta 103 sun tarwatsa wata maboyar ‘yan ta’addan na IPON/ESN a dajin Nkwere Inyi dake karamar hukuma Ijo River a jihar Enugu.

Sai dai a yayin atisayen ‘yan Ta’addan sun tsere zuwa daji, nan dakarun sojin suka sami nasarar kwato mota kirar Toyota Highlander SUV da ake zargin mallakin miyagun ce, sauran kayayyakin da aka kwato sun hadar da Babura biyu, bindiga kirar double barrel guda daya da kuma alburusai masu rai da dama.

Daga bisani sanarwa ta bukaci al’ummar yankin su tallafawa dakarun sojin da sahihan bayanai kan ayyukan ‘yan ta’addan.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 17 hours 34 minutes 50 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 16 minutes 15 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com