Alkalin Alkalan Nijeriya Yayi Murabus

Alkalin Alkalan Nijeriya (CJN) mai shari’a Muhammad Tanko yayi murabus daga mukamin sa na babban mai shari’a a kotun koli.

Rahotannin sun bayyana cewa ya yi murabus din ne sakamakon rashin lafiya  da yake fama da ita.

Ana sa rana daga na zuwa ko wanne lokaci za’a maye gurbin sa da mai shari’a olukayode Ariwoola , wannan da ke matsayin mafi girma bayan mai shari’a Mary Odili wadda tayi ritaya  12 ga watan mayun bayan ta cika shekaru 70 a matsayin mukaddashi.

An dai hafi Mai shari’a Muhammad a garin Doguwa, dake karamar hukumar Gaide ta jihar Bauchi a ranar 31, Disamban 1953.

Ya halarci makaranatr Firamare ta Giade daga 1961 zuwa 1968, inda ya tafi zuwa sakandire ta Azare a shekarar 1969 zuwa 1973, daga bisani  ya zuwa makarantar Abdullahi Bayero University College, kano inda yayi karatun share fagen shiga jami’a na IJMB daga shekarar 1975 zuwa 1976, bayan ya sami nasarar ne ya sammi gurbin karatu a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria daga shekara 1976 zuwa 1980, ya kuma halarci kwalejin  koyan aikin shari’a daga shekarar 1980 zuwa 1981.

Domin Karin karatu ya koma zuwa jami’ar Ahmadu Bello dake Zari’a, inda ya sake samun digiri na 2 a fannin shari’a (LLM) a wani tsari na wucin gadi daga shekarar1982 zuwa 1984.

Saboda sake samun gogewa a fannin ya dora dai a jami’ar ta Ahmadu Bello domin samu digirin na 3 (PhD) a fanin shari’a duk dai a tsarin wucin gadi.

Daga bisani shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da shi a matsayin Alkalin Alkalan kasar a watan Janairun 2019, bayan dakatar da mai shari’a Walter Onnoghen.

Bisa doka dai dukkan babban Alkalin kotun koli a Nijeriya wajibi ne yayi murabus da zarar ya kai shekara 70 a duniya.

By PRNigeria

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 35 minutes 14 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 11 hours 16 minutes 39 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com