Dakarun Sojin Nijeriya Sun Tarwatsa Maboyar ‘Yan Ta’adda A Jihar Benue

Dakarun sojin Nijeriya karkashin WHIRL STROKE sun sami nasarar kame wata mota mai lambar Abuja KWL 846 XB makare da yankakkun tsaffin karafunan layin dogo akan hanayar Udei zuwa Makurdi lafiya, gami da wasu mutum 7 dake cikin motar.

Wannan na cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran rundunar sojin Nijeriyar ya Manjo Janar Bernar Onyeuko ya fita a wani bangare na bayyana irin na sarorin da rundunar ke samu wajen kawar da ayyukan ‘yan ta’adda a fadin kasar.

Sanarwar tace tuni aka mika motar da mutun 7 dake cikin ta da ake zargin su da aikata laifin ga hukumomin da suka dace domin fadada bincike.

Haka kuma dakarun na WHIRl STROKE sun sami nasarar kama wani mutum mai suna Mista Ardo Manu Abdulrahman wanda take zargi da bada hayar makamai ga ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane da sauran aikata laifuka a jihar Taraba.

A yayin sumamen rundunar ta sami nasarar kwato wayoyin hannu guda 4 da kudi naira Dubu Saba’in da Hudu da dari uku da arba’in (74,340.00), haka kuma a wani sumamen makaman cin wannan a wata maboyar ‘yan ta’addan a Maraba a mazabar Ukyongun Ityuluv na karamar hukumar Ukum dake jihar Benuwai dakarun sun sami nasarar kama wani mutum Mista Ichen Gbaka da matasar Uwargida Saloma Gbaka da suke hada baki da ‘yan ta’addan.

Sanarwa ta kara da cewa a ranar 24 ga watan Yuni 2022 dakarun sun sami nasara kame wasu masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa su hudu (4) a mazabar Igumale dake karamar hukumar Ado ta jihar Benuwai, wanda tuni suka mika su hannun jami’an ‘Yan Sanda.

A ranar 26 ga watan Yuni, 2022 dakarun soji suka gudanar da wani sumame amaboyar ‘yan ta’addan dake  kauyen Mbahuwuhe dake karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar ta Benuwai, a yayin sumamen an halaka ‘yan ta’adda uku (3) tare da kubutar da wanda sukayi garkuwa da shi Auya Tisa, yanzu haka yana karbar magani gami da kulawar likitoci, tare da kwato babur din hawa guda daya (1) wayoyin hannu guda biyu (2) kafin kwato kayan sai da dakarun suka fatattaka maboyar ‘yan bindigar.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 21 hours 46 minutes 6 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 27 minutes 31 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com