Home Labarai Gwamnan Jihar Osun Adegboyega Oyetola ya Mika Ta’aziyyar Sa Bisa Rasuwar Imam...

Gwamnan Jihar Osun Adegboyega Oyetola ya Mika Ta’aziyyar Sa Bisa Rasuwar Imam Agaka

Gwamnan jihar Osun Adegboyega Oyetola, ya mika sakon ta’aziyyar sa ga babban mai tace labarai na Jaridar PRNigeria da Economic Confidential Malam Yusha’u shu’aib, bisa rasuwar mahaifin sa, Imam Abdulhameed Shuaib Agaka.

Wannan dai na cikin wata wasikar mai dauke da sa hannun Gwamnan, wadda ke bayyana Imam Agaka matsayin wata taska da Al’umma ke kwasar romon ilimi, baya ga sadaukar da kai wajen yiwa kasa da Al’ummar ta aikin daya kama, wadda kuma hidimar zata zama abin koyi ga masu tasowa anan gaba.

Shahararren malamin ya rasu ne kwanan nan kuma tuni  aka yi masa sutura (binne shi) bisa tanadin addinin musulunci, a garin Ilori dake jihar kwara.

Ta cikin wasikar da mai Magana da yawun sa Isma’il Omipidan, ya kawo kafa da kafa Shalkwatar jaridar ta PRNigeria dake Birnin Abuja, Gwamnan ya bukaci Malam Yusha’u ya dauki danga tare da koyi da irin rayuwar da mahaifin sa yayi kasancewar sa fitaccen mai Ilimi wanda ke amfani da ilimin yadda ya kamata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp