Dakarun sojin dake aikin wanzan da zaman lafiya a yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya na Opration HADIN KAI sun sami nasarar halaka ‘yan ta’adda masu tarin yawa, kame wasu gami da kubutar da mutanen da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su tare da kwato makamai.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran rundunar sojin na kasa Manjo janar Bernard Onyouko ya fitar, wandda tace a kokarin da dakarun sojin Nijeriyar ke yin a ganin sun samar da sahihin zaman lafiya sun kara kaimi wajen gudanar da ayyukan su a garuruwan Buduwa, hanyar Bama zuwa Pulka, kauyen Tuwe, hanyar Kondugazuwa Kawuri, garin Brema dake Damboa Motor Park, Tashangoto, Benishek, Kukaneta dukkan su a jihar Borno.
Read Also:
Sanarwa ta kara da cewa a ranar 17 da 18 ga watan Yuni, 2022 bataliya ta 152 a kauyen Buduwa dake karamar hukumar Bama ta jihar Borno, a wani artabu tsakanin dakarun sojin Nijeriya da mayakan kungiyar boko Haram tsagin ISWAP dakarun sojin sun sami nasarar halaka mayakan Boko haram 7 yayin da kuma suka halaka barayin Shanu 14 suka kuma kwato kekunan hawa 3.
Haka kuma rundunar ta sami nasarar kama wasu dake hada kai da ‘yan boko haram wajen sama musu kayan Aiki, wanda suka hada da Malam Abach Usman a garin Benshek da kuma wani dan ta’adda daya shahara wajen samar da manfetur ga ‘yan ta’adda mai suna Malam Ibrahim Gira.
Ta cikin sanarwar rundunar ta bayyana cewa yanzu haka dai dakarun nata sun sami nasarar hallaka ‘yan Boko haram 11, tare da kame 11, sannan kuma sun kame barayin shannu 14, gami da kwato bindiga kirara AK47 guda 2, kekune 3, bindigu kirar gida guda 2 da kuma Alburusai masu tsayin mita 7.62mm guda 90 da mota kirar Gulf guda 1.
Haka kuma mambobin kungiyar ta boko haram na cigaba da mika wuya tare da ajje makaman su daga 1 zuwa 15 ga watan Yuni rundunar ta sami nasarar karbar mutum 4,770 wanda suka hadar da maza 864 mata 1,415 da kananan yara 2,490.
Daga bisani sanarwa tace dukkan mayakan kungiyar ta ISWAP da iyalan su da suka mika wuya an killace su, haka kuma dukkan wadanda aka kama an mika su ga hukumomin da suka dace.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 16 minutes 32 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 22 hours 57 minutes 57 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com