Akalla fararen hula mutum 43 ne suka mutu wanda suka hadar da sojojin 30 da ‘yan sandan kwantar da tarzo 7 sakamakon harin ‘yan bindiga a wani wurin hakar ma’adanai a karamar hukumar Shiroro dake jihar Nijer, kamar yadda wata majiya ta shaida mana.
A yayin da gwamnatin jihar ta Niger ke tabbatar da faruwar harin, ta bayyana cewa bata kai ga gano adadin wadanda harin ya rutsa dasu ba.
Mazauna yakin sun bayyana cewa jami’an Bincike sun gano gawarwakin sojoji da Jami’an ‘yan sandan 37 yashe a cikin daji ranar Alhamis, gami da gawarwakn fararen hula 6 duk a cikin dajin.
Read Also:
Mazauna yankin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da ‘yan Nijeriya da ‘yan kasar Sin (Chaina) da dama a yayin harin da suka kai wajen hakar ma’adanan a ranar laraba.
Yusuf Kokki, wanda gudana ne cikin shuwagabannin kungiyar Matasan Shiroro, ta cikin wata sanarwa da ya aikewa manema labarai yace mazauna wurin sun shaida harin maharan dauke da muggan makamai.
Ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne yayin da ‘yan bindigar suka yiwa wurin hakar ma’adanan tsinke, nan suka fara harbi kan mai uwa da wabi akan ma’aikatan da masu tsaron lafiyar su.
Ya ce mazauna yankin zasu zakulo Karin wasu gawarwakin a aikin da suke cigaba da yi na nemo wadanda harin ya rutsa dasu.
Yace jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma 7 sun mutu da wasu Karin fararen hula guda 6 a wajen hakar ma’adanan.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 2 minutes 22 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 43 minutes 47 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com