Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da bullar cutar Kyandar biri karon farko a jihar, kuma sun masa magani sun sallame shi.
Kwamishinan lafiya na jihar Yakubu Danja, ne ya tabbatar da bullar cutar yayin da yake gabatar da fara rabon magungu kyauta a kananan hukumomi 34 dake fadin jihar.
Yace sun sami mutum 15 da ake zargin suna dauke da cutar kuma an dauki samfurin gwajin zuwa birnin tarayya Abuja, wanda yanzu haka ana sauraren sakamako.
Read Also:
Danja ya kuma bayyana cewa za’a raba magungunan kyauta ga cibiyoyin bada maganin a jihar, kana Gwamnatin ta himmatu wajen wayar da kan dukkan kungiyoyin bada Agajin gaggawa domin dakile yaduwar Cutar.
Ya kara da cewa daga cikin magungunan da aka raba domin dakile yaduwar cututtuka har da maganin cutar kwalara da sauran cutattukan dake da alaka da zuwan yanayin damuna.
Daga bisani kwamishinan ya zaga cibiyar bayar da Agajin gaggawa inda ya mika na’urar Firinji guda140 domin Ajje alluran, ya kuma tabbatar da cewa hukumar lafiya matakin farko ce ta bayar da su kyauta.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 32 minutes 41 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 14 minutes 6 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com