Rahotannin na bayyana cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci gidan Gyaran Hali na Kuje da ke birnin tarayya kasar bayan harin da aka kai gidan ranar Talata da daddare.
ko da yake dai Kawo yanzu babu cikakken bayani kan abubuwan da shugaban ya yi a ziyarar da ya kai.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sai dai ta cikin wata sanarwa ta baya- bayannan da hukumar dake lura da gidajen Gyaran hali ta kasar ta fitar kuma ta aikewa PRNigeria sun bayyana cewa mutum 879 ne suka tsere daga gidan Gyaran halin, harin da ake zargi mayakan Boko Haram ne sun kai.
Sanarwar da mai magana da yawun gidan-yarin, Abubakar Umar ya sanya wa hannu, ta ce wasu fursunoni sun koma don radin kansu amma kawo yanzu ana neman fursunoni 443.
wannan ziyara tazo wa Al’ummar kasar a ba zata kasancewar sanarwa ta gabata shugaban na shirin yin balaguro zuwa kasan Senegal.












