Yadda Firsunoni 879 Suka Gudu Daga Gidan Gyaran Hali a Nijeriya

Hukumar dake lura da Gidajen Gyaran hali ta Nijeriya ta tabbata da cewa DCP Abba Kyari da wasu wadanda ake basu kula ta musamman a gidan gyaran hali na kuje dake birnin tarayya Abuja basu tsere ba.

Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin hukumar CSPC Umar Abubakar AICMC, ANIPR., wadda aka aikewa PRNigeria, amadadin babban kwantirolan hukumar.

Wannan dai na zuwa ne tun bayan wani hari da ake zargin mayakan kungiyar tada kayar baya na boko haram sun kai gidan gyaran hali na Kuje dake birnin tarayya Abuja,

Sanarwar tace fursunoni 879 ne suka tsere daga wurin a lokacin da maharani suka musu dirar mikiya, said ai ya zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto an sami nasarar kamo 551 inda kuma 443 suka dawo don radin kansu, baya ga fursunoni 4 da suka rasa rayukan su, in da fursunoni 16 suka sami muggan raunika kuma yanzu haka suna karbar kulawa ta musamman, inda tace ana kuma ci gaba da kokarin nemo sauran firsunonin.

Haka kuma hukumar ttace ta girki jami’an ta na sashen bayanai (CIMS) tare da hadin gwuiwar jami’an hukumar samar da katin shaidar zama dan kasa (NIMC) domin bin diddigin duk fursunonin da suka gudau tare dadawo da su gidan gyaran halin.

Sannan kuma sanar tace hukumar na amfani da wannan dama wajen tabbatarwa da jama’a cewa DCP Abba Kyari da sauran manyan jami’an tsaro da ake tsare da su a wajen basu gudu ba, a halin yanzu suna hannun hukumar cikin koshin lafiya.

Idan dai za’a iya tunawa, tun bayan harin da aka kai cibiyar gyaran hallin ta Agbolongo dake jihar Oyo, ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya gana da shuwagabannin hukumomin tsaro dake karkashin sa, domin yin hadin gwuiwar jami’an da suka kunshi na hukumar Gyaran Hali ta kasar, hukumar dake lura da shige ta fice da kuma hukumar tsaron ta civil Defence, hukumar tsaro ta Farin kaya DSS, da kuma rundunar sojojin kasar, domin dakile ci gaba da samun irin wannan matsala.

Sanarwa ta kara da tabbatar da cewa a yayin artabun da jami’an dake tsaron gidan gyaran halin sun sami nasarar hallaka da dama cikin su, yayin da wasu suka tsere da raunin harbin bindiga.

Daga bisani hukumar ta bukaci Asibitoci da sauran cibiyoyin kiwon lafiya da likitoci su kai rahoton duk wanda ya zo wurin su don jinyar raunin Harbin bindiga ga hukumomin tsaro mafi kusa.

Sanarwa ta Ambato babban kwantirolan hukumar ta gyaran Hali Haliru Nababa FICMC, mni na yabawa da kokarin sauran jami’an tsaron bisa kai daukin gaggawa akan lokaci, ya kuma yi kira ga jama’a da su taimaka da sahihan bayanan da zasu taimake su wajen kame sauran firsunonin da suka tsere.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 12 hours 37 minutes 52 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 19 minutes 17 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com