Wata gidauniya mai lakabin Gidauniyar dashen Koda, guda cikin kungiyoyi masu zaman kansu (NGO’s) ta bayar da tallafin kayan aikin dashen koda ga asibitin kwararru na Muhammad Abdullahi Wase da ke jihar Kano a Arewacin Nijeriya.
Wani bincike na PRNigeria na baya-bayan nan ya nuna yadda rayuwar masu fama da ciwon koda da dama a Kano ke dogara da injinan wankin kodar koda 12 kacal a manyan cibiyoyin kiwon lafiya guda biyu da suka hadar da Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da Asibitin kwararru na Abdullahi Wase.
A Asibitin kwararru na Abdullahi Wase a kalla majinyata dake da nasaba da koda, 160 ke ziyartar asibitin duk mako, haka akan sami sabbin masu kamuwa daga cutar mutum 15 dake zuwa duk makon.
Yayin da a Asibitin koyarwa na Aminu Kano akan sami majinyata kusan 70 a duk mako dake zuwa domin wankin kodar. Amma akalla ana ganin masu fama da cutar mutum 40, baya ga yadda da dama ke zaman jira.
Duk da tsadar wankin na koda, wasu daga cikin injinan wankin basa aiki yadda ya kamata.
Read Also:
Da yake jawabi a yayin mika kayayyakin aikin ga asibitin shugaban gidauniyar dashen kodar, Alhaji Ibrahim Abdullahi ya ce sun dauki wannan mataki ne domin rage radadi gami da wahalhalun da masu fama da lulurar ke fuskanta.
Ya kara da cewa sun dauki matakin tallafawa Asibitin na Abdullahi Wase ne sakamakon kokarin sa rage farashin kudin wankin koda ga masu fama da lalurar.
“Mun kashe sama da naira dubu dari biyar domin samar da kayan aikin wankin koda, don haka muna kira ga wasu kungiyoyi da masu hannun da shuni da suyi koyi da wannan abun Alkhari.
A nata jawabin, tsohuwar Ministar ilimi ta Nijeriya, Farfesa Rukayya Ahmad Rufa’I, wacce mamba ce a gidauniyar ta yi kira ga gwamnatin Jihar Kano da ta gaggauta daukar matakai domin magance kalubalen da asibitin ke fuskanta.
Babban Daraktan asibitin wanda ya sami wakilci Dr. Bashir Garba Ahmad ya yaba da irin hangen nesa da jajircewa da wannan gidauniya ta yi wajen rage radadin ga masu fama da lalurar.
Ya kara da cewa Asibitin na fuskantar kalubale masu tarin yawa, musamman na kayan da suka jibanci ayyukan lura da masu famada lalura koda, wanda ke bukatar gwamnatin jihar kano da masu ruwa da tsaki su gaggauta daukar mataki.
By PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 17 hours 3 minutes 54 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 45 minutes 19 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com