Bincike: Shin da Gaske ne Dan Peter Obi Yataka Tutar Nijeriya, Yana Sanye da Kayan Kungiyar ‘Yan Awaren ta Biyafara? 

KORAFI: Wani rubutu dake dauke da hoton wani matashi sanye da kayan kungiyar dake rajin kafa kasar Biyafara, ya taka tutar Nijeriya, ya yadu a kafar sada zumunta, wadda ake ikirarin matashin Da ne ga Peter Obi.

CIKAKKEN BAYANI: Hoton ya bayyana wani Matashi mai hasken fata, sanye da karamar riga mai dauke da Ruwan kalar tutar ‘Yan Awaren biyafara ya kuma taka tutar Nijeriya.

Da dama cikin masu Amfani da kafar sada zumunta ta zamani sun yi ikirarin cewa wanda ya taka tutar Da ne ga Dan takarar shugabancin Nijeriya karashin Inuwar Jam’iyyar Labour Party (LP). Peter Obi

Wasu cikin rubututtukan sun bayyana cewa “Wannan Dan Peter Obi ne, kuma dan kungiyar IPOB ne gashi ma sanyi da kayan su, kalli yadda yake taka tutur Nijeriya kuma mahaifin sa ne ke neman takarar shugabancin Nijeriya.

Wani sakon hoto da aka sake sanyawa a kafar Twitter wanda aka rubuta “a cikin wannan Hoton Gegory Peter Oseloka Obi, da ga Mista Peter Obi Sanye da kayan Kungiyar IPOB, yana tsaye kan tutar kasar Nijeriya, nayi imanin cewa kungiyar IPOB/UBM ne ke daukar nauyin Peter Obi, za’a lalata Nijeriya a kunna mata wuta (SIC).”

Haka mutane da dama sun yada hoton da mabambanta kalamai a kafafen sada zumunta.

Peter Obi dai tsohon Gwamnan jihar Anambra ne kuma dan takarar shugabancin Nijeriya a kakar zabe mai zuwa karkashin inuwar jam’iyyar Labour Party (LP).

BINCIKEN TABBATARWA: A binciken kwakkwafi da PRNigeria tayi wa hoton da ake yadawa a kafafen sada zumuntar, ta yiwa hoton duban kurulla, inda ta gano motocin dake kusa da wanda ya aikata taka tutur Nijeriyar, mallakin hukumar ‘yan sandan kasar Jamus ne haka kuma alamu sun tabbatar da ‘yan sandan dake tsaye a wajen ‘yan sandan kasar Jamus ne, yayin da Dan mista Peter Obi, Oseloka Obi ya kasance yana birnin London ne ba a Jumus yake ba.

Domin sake samun Wasu shaidu da zasu kara tabbatar maka da gaskiya lamarin na ka bincika nan

Hazakali, Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ya nisanta Dansa daga haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB).

Ta cikin wata tattaunawa da kafar talabishin ta Arise TV a ranar Laraba, Obi yace Dansa mutum ne wanda yasan me yake wanda yanzu haka yake “gudanar da aiki a birnin London”.

Yace “akan batun Da na, wancen matashin ba Da bane. Da na kwararre ne wanda yanzu haka yake aiki domin dogaro da kan sa, bari na fada muku wani abu, ban dade da dawowa daga birnin Landan na kasar burtaniya ba, ban san ya shi a ido na ba saboda aiki daya sha masa kai, ya fada min baba ya kake? ya siyasa, ya kuma yakin neman zabe? Ina jin dadin yadda kake gudanar da al’amuranka.

“Idan zan nuna maka tattaunawar da mukayi ta sakon karta kwana zaka ga yadda ya fada min cewa kaga baba, bani da lokacin wannan Magana.”

“Idan har zan kasa ganin Da na saboda aiki daya sha masa kai. To kaga kuwa bashi da lokacin aikata wannan aiki, Da na yana rayuwa a kasar Burtaniya. Zan kuma iya biyan ko nawa ne ga dukkan wanda zai tabbatar mu da cewa wanda ya aikata wannan aiki Da na ne.”

Haka kuma daraktan yada labarai na Peter Obi ya wallafa wani sako a shafin sa na Twitter wanda yake cewa “Muna so mu bayyana cewa wancen matashin da ake Magana a kai ba Da bane ga Peter Obi, domin shi ya fahimci dukkan abinda ya kamata ya gudanar, yana da cikakkiyar tarbiyya.”

Haka kuma sanarwa ta kara da cewa “shi fa Oseloka Obi na da tsayin daya kai kafa (6) kuma yafi wannan matashin tsayi, domin wannan matashin daya aikata wanna dabi’a tsayin sa bai kai kafa 5 ba.

“Ta cikin sanarwa ya kuma yi kira ga masu neman mukaman siyasa, da magoya bayan su da suke koyi da dabi’u kyawawa a ko wanne lokaci.

KAMMALAWA: Babu wata shaida da ta tabbatar da cewa dan fafutuka IPOB da ya taka tutar Nijeriya wanda ke sanye da kayan masu launin kungiyar masu fafutukar kafa kasar biyafara wanda kawo yanzu ba’a san ko wanene ba, dan Peter Obi ne, binciken da PRNigeria ta gudanar ya tabbara da cewa an sauya labarin ne.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 4 hours 36 minutes 41 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 6 hours 18 minutes 6 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com