Home Labarai BINCIKE: Shin Gaskiya Ne Tsakanin Shekarar 2010 Zuwa 2018 An Yi Tikitin...

BINCIKE: Shin Gaskiya Ne Tsakanin Shekarar 2010 Zuwa 2018 An Yi Tikitin Kirista – Kirista A Jihar Ekiti?

KORAFI: Akwai wani rubutu dake yawo a kafafen sada zumunta na zamani (Facebook) cewa a jihar Ekiti an yi tikitin Kirista – Kirista daga shekarar 2010 – 2018.

CIKAKKEN BAYANI: A cikin wani shafin facebook; mai Suna Buharist Reporter, an wallafa wani rubutu a ranar 30 ga watan Yuni, wanda ke kunshe da jerin jadawalin ‘yan siyasar da suka gabata wadanda suka taba yin takarar shugabancin Nijeriya ko kuma gwamna a wata jihar da suka dauki mataimakin su daga cikin mabiya Addini Kirista, rubutun da aka yiwa lakabi da “FLASHBACK CHRISTIAN-CHRISTIAN TICKET”  ya Ambato sunan Mista Ayo Fayose wanda ya Mulki jihar Ekiti daga shekarar 2014 zuwa 2018 tare da mataimakin sa, Niyi Adebayo, tikitin Kirista-kirista ne amma Al’ummar Musulmi basu ce komai kan lamarin ba.

Haka kuma shafin ya mabato sunan Gwamna Kayode Fayemi na Ekiti tsakanin shekara 2010 zuwa 2014 ya dauki kirista a matsayin mataimaki sa.

BINCIKEN TABBATARWA: PRNigeria  ta gudanar da wani bincike da ya tabbatar mata da cewa Dr. Kayode Fayemi da Mr Ayo Fayose sun gudanar da tikitin kirista – kirista a yayin da suke takarar zaman gwamnan jihar kuma bayan gudanar da zaben sun sami nasarar.

A tsakanin shekarar 2010 zuwa 2014, Dr Kayode Fayemi ya dauki Kirista a matsayin wanda zai masa mataimaki, Funmilayo Olayinka karkashin Inuwar jam’iyyar (ACN), wanda daga bisani ya mutu a ranar 6 ga watan Afrilun 2013.

Ta cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 3 ga watan Mayu, shekarar 2013, yayin da yake jawabi ga kakakin majalisar dokokin jihar Adewale Omiri, ya bukaci majalisar ta aminci da nadin farfesa Modupe Adelabu, wanda shima mabiyin addinin kirista ne, matsayin mataimakin Gwamnan jihar, domin cike gurbin mataimakin gwamnan jihar da ya mutu.

Haka kuma Ayo Fayose ya gudanar da tikitin kirista-kirista tsakanin shekarar 2014 zuwa 2018 a karkashin inuwar jam’iyyar “People Democratic Party” PDP. Inda ya dauki Farfesa Kolapo Olusola Eleka, wanda shima mabiyin addinin kiristanci ne.

KAMMALAWA: Sakamakon bayanan da PRNigeria ta tattara a jihar ya tabbatar mata da cewa Mista Ayo Fayose da Dr. Kayode Fayemi sun gudanar da tikitin Kirista-kirista a mabambanta lokaci a jihar ta Ekiti.

By PRNigeria

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba Hatsarin Jirgin Sama na Ondo: Disu Ya Jajantawa NAF, Ya Jaddada Goyon Bayan Ƴan SandaHukumar Kwastam ta Kwace Wiwi ta N3.67bn da Aka Boye a Cikin Motocin da Aka Shigo da su, da Sauran Kayayyaki a Tashar Jirgin Ruwa ta Legas
X whatsapp