Gabatowar kakar zaben 2023, kungiyar Kiristoci ta Nijeriya wato (CAN) dake fadin jihohi 19 na Arewa gami da birnin tarayya Abuja ta bukacin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, kan ta tabbatar da zaben 2023 ya kasance sahihin zabe mai cike da adalci.
Haka kuma kungiyar ta bukaci shugaban kasa Muhammad Buhari, da ya bayar tarihi mai kyau bayan ya sauka daga karagar Mulki ta hanyar tabbatar da kyakkyawan sauyi a shekarar 2023.
Wannan na kunshe ta cikin wata takardar bayan taron majalisar zartarwar kungiyar a jihar kaduna, taron bisa jagorancin shugaban kungiyar reverend Yakubu Pam da sakataren kungiyar Elder Sunday Oibe, inda sanarwar tace wadanda ke kassara tattalin arzikin kasa zasu yi amfani da yunwa matsayin makami a babban zaben 2023 mai zuwa.
Kungiyar ta bukaci Gwamnati a kowanne mataki data dauki gabarar magance dukkan matsalolin talauci da yunwa dake addabar Al’umma Nijeriya.
Read Also:
“Muna kira ga Al’umma Nijeriya dasu tabbar an gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da tashin hankali ba. zabe ba yaki bane. Babu wani dan siyasa da zai yadda ya mutu, don haka kada kowa ya dauki doka a hannun sa.
“Dole ne ‘yan siyasa su gudanar da harkokin sun a siyasa bisa tanadin doka da oda, ba tare da nuna kyama ba, dole ne shuwagabanni jam’iyya, ‘yan Takara, ‘yan jam’iyya , magoya baya, su mayar da hankali yayin yakin neman zaben su da kalaman da zasu taimaka wajen magance kalubalen dake addabar kasa nan.
“Kungiyar CAN ta reshen Arewa na kira ga matasa, kada su yadda wani dan siyasa yayi amfani da su wajen tada husuma, idan kun lura ‘ya’yan sun a can suna karatu a ketare, ya kamata iyaye su ja kunnen ‘ya’yan su da kada ‘yan siyasa su dauke si aiki a matsayin ‘yan daba,” inji sanarwar.
Haka kuma kungiyar ta nuna damuwar ta kan yajin aikin kungiyar malaman jami’oin Nijeriya ta ASUU da ya dauki lokaci, inda tayi kira ga Malaman da Gwamnatin tarayya kan su samar da matsaya guda domin cigaban dalibai.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 23 minutes 43 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 5 minutes 8 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com