Bagudu: Najeriya na Bukatar Masu Zuba Jari a Duniya don Habaka Tattalin Arziki

Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya ce Najeriya na bukatar hadin gwiwar zuba jari a duniya domin gina tattalin arzikinta, inda ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa masu fata na gari duk da kalubalen da kasar ke fuskanta.

Bagudu ya hori ‘yan kasar da kada su yanke kauna ko kuma su karaya game da yadda basussukan kasar ke ciki wanda ka iya zama dalilin da zai sa Al’ummar kasar su yanke tsammani.

Hakan ya zo ne a daidai lokacin da takwaransa na jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya shawarci gwamnan jihar Ekiti mai jiran gado, Biodun Oyebanji, da ya inganta ci gaba ta hanyar gina gadon magabacinsa.

Gwamnonin sun yabawa gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi bisa yadda ya samar da amana tsakaninsa da mutanen Ekiti, ta hanyar gudanar da kyakkyawan shugabanci da ya shafi kowane bangare na tattalin arziki.

Sun yi magana ne a Ado Ekiti, jiya a wani taron kasa da kasa da aka gudanar don karrama Fayemi mai taken: “JKF: A Journey in Leadership”.

Bagudu ya ce, “Hatta manyan kasashe irinsu Amurka, wadanda sun fi Najeriya ci gaban tattalin arziki, sun ma fi Najeriya bashi. Abin da muke bukata yanzu shine saka hannun jari ta hanyar haɗin gwiwar duniya sama da mutane miliyan 200, don gina tattalin arzikinmu da gina jama’armu.”

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 14 hours 56 minutes 14 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 37 minutes 39 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com