An Bude Yin Rijistar Shiga Gasar 30 Under 30

An bude yin rijistar Karrama zakakuran matasa 30 ‘yan kasa da shekaru 30 da za’a gudanar karon farko a jihar Kano.
Kafar yada labarai ta Arewa Agenda hadin gwuiwa da Jaridar PRNigeria da Daily Nigerian sun samar da wani dandamali na karrama matasa 30 ‘yan kasa da shekaru 30 mai lakabin Arewa Star Awards (ASA2022).
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da shugaban jaridar Arewa Agenda Muhammad Dahiru Lawal ya fitar, inda yace babban taron bada lambar yabon za’a gudanar da shi ne cikin watan Disamba a jihar kano, taron da zai zama wurin haduwar manyan mutane daga yankin na arewacin Nijeriya, masu fada aji gami da masu hannu da shuni da wadanda karan su yakai tsiko a fadin Nijeriyar.
An samar da wannan bikin domin zakulu wasu fitattun matasa hazikai dake ‘yankin Arewacin Nijeriya guda 30 wadanda kuma ke da shekaru kasa da 30 da haihuwa dake gudanar da ayyuka masu inganci da tasiri a sassa daban-daban da suka jibanci rayuwar Dan Adam.
Kyautar Arewa Stars Award “data hada hazikan matasa” zata karrama matasa 30 wadanda basu wuce shekaru 30 ba, inda zasu karbi kyaututtuka 30 a fannoni 30 da suka hadar da Sadarwa, Ilimi, Siyasa, kafar sadarwa ta zamani, Ado da kwalli, Nishadi, fintech, shari’a gami da kirkira.
Sauran bangarorin sun hadar da sana’oin dogaro da kai, Magunduna (kiwon lafiyar Al’umma) aikin Banki, Adon gidaje, Jogoranci, wasanni, Zanen Gini da kere-kere.
Sauran sun hadar da; Jaruman wasan kwakwaiyo mata da Maza, masu zane-zane damasu zaden Abu mai Mutsi, zakakurai a fannin tallafawa Dan Adam, masu kwalliya da Ado. Sana’oin Hannu (takalma, Jaka, Rini) rajin kare hakki/aiki da harkokin sanarwa da fasaha gami da gidaje.
Babban taron karramawar zai kunshi
Muhimman taron zai gabatar da bayar da kyauta ga matasa 30 dake kasa da shekaru 30, kwarya-kwaryar tattaunawa, bajakolin Fasaha, kyautar girmamawa ga jagorori da masu ayyukan tallafawa Al’umma, girmama wasu kungiyoyi, Nishadantar, (mawaka da jaruman wasan kwaikwayo) liyafar cin abincin Dare da kuma kaddamar da littafin Labaran karyar 101 kan zanga-zangar EndSARS da aka fassara zuwa harshen Hausa.
Masu shiga za su iya zabar kungiyoyi, daidaikun mutane da masu ba da Agaji dake tallafawa matasa don samun lambobin na girmamawa.
Wadanda suka lashe babbar kyauta daga ko wanne nau’I za su zama jakadunmu don ci gaba mai dorewa kuma za’a yi musu lakabi da “Taurarin Arewa.”
Za’a rufe shiga wannan gasa a ranar 8 ga watan Nuwamba, 2022 za’a fara zaben wadanda suka yi nasara mako guda bayan fidda sunayen wadanda suka yi nasara daga kwamitin alkalan gasar.
Kwamitin Alkalan ya kunshi kwarrun masu bada agajin jin kai, malamai da masana a harkokin masana’antu
Domin samun damar shiga wannan gasar ta karrama matasa 30 ‘yan kasa da Shekaru 30 a ko wanne fanni sai a bi: https://bit.ly/3rKdxiF.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 15 hours 14 minutes 29 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 55 minutes 54 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com