Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta ɗauki matakin dakatar da kowace irin hada-hada a wasu yankunanta da ke fama da matsalar tsaro.
wannanna kunshe ne ta cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar a ranar Juma’a, ta ce ta lura da yadda ake samun taɓarɓarewar tsaro ta hanyar sace-sacen al’umma a kauyuka da kuma kan wasu hanyoyin jihar.
A saboda haka sanarwar ta ce gwamnati ta kulle, ƙananan hukumomin Anka da Bukuyum da kuma Gummi ɗungurungum.
Sauran kauyukan da kullewar ta shafa su ne Ƴarkofoji, da Birnin Tudu, da Rini, da Gora Namaye, da Janbako, da Faru, da Boko da kuma Mada.
Read Also:
Sanarwar ta kuma ce daga yau an rufe kasuwannin Danjibga da Bagega, Bugu da ƙari an dakatar da zirga-zirga kan hanyoyi da suka hadar da Colony zuwa Lambar Boko, Bakura zuwa Lambar Damri, Mayanchi zuwa Daki Takwas har zuwa Gummi, Daki Takwas zuwa Zuru, Kucheri zuwa Bawaganga zuwa Wanke, Magami zuwa Dangulbi sai kuma Gusau zuwa Magami
Gwamnati ta ce an ɗauki matakin ne domin bai wa jami’an tsaro damar gudanar da ayyukansu ba tare da wani cikas ba.
Ta kuma ce ta bai wa jami’an tsaro umurnin ɗaukan mummunan mataki kan duk wanda aka samu da laifin karya dokar.
jihar Zamfara na guda cikin jihohin Arewa maso yammacin Nijeriya da matsalar tsaro kekara karama sakamakon ƴanfashin daji da ta fi kassarar jihar dama yankin.
PRNigeria Haus
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 3 minutes 22 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 44 minutes 47 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com