Home DUNIYA Al’shabab ta sake kai hari wani Otal a Somalia

Al’shabab ta sake kai hari wani Otal a Somalia

Wasu rahotanni na bayyana cewa akalla mutane 3 sun rasa rayukansu, sannan da dama sun jikkata sakamakon wani hari da aka kai da mota makare da bama-bamai da kuma harbe-harben bindiga kan wani otel da ke birnin Kismayu na kasar Somalia.

An fara jin karar harbe-harben bindiga jim kadan da fashewar bama-bamai da ke cikin motar wadda ta  yi karo da babban kofar shiga cikin otel din na Tawakal, yayin da mayakan Al-Shebab masu alaka da Al-Qaeda suka dauki alhakin kaddamar da farmakin.

Rahotanni na cewa, an kai farmakin ne a daidai lokacin da ake kan gudanar da wani taro a otel din kan yadda za a murkushe mayakan na  Al-Sshebab a kasar ta Somalia.

Har yanzu dai kungiyar ta Al-Shebab na rike da ikon wasu yankuna na birnin na Kismayu mai cike da hada-hadar kasuwanci a yankin kudancin Somalia.

Sojojin kasar sun yi nasarar fatattakar mayakan na Al-shebab daga birnin a shekara ta 2012, birnin da ke samar wa mayakan kudaden shiga domin sayen makamai.

Ko a shekara ta 2019, sai da mayakan suka kaddamar da makamancin wannan harin da ya kashe mutane 26 a Kismayu.

Har yanzu dai mayakan Al-Shebab ba su daddara ba a yunkurinsu na ganin sun kifar da gwamnatin Somalia domin kafa irin tasu gwamnatin, yayin da suka kashe dubban ‘yan kasar a jerin hare-haren da suka kaddamar cikin shekaru 10.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp