Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce jami’anta sun kama wani ɗan Nijar da ‘yan Pakistan biyu bisa zargin safarar koken.
A sakon da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce an kama ‘yan Pakistan din a filin jirgin sama na Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya, yayin da aka kama ɗan Nijar ɗin a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin ƙasar
Read Also:
Hukumar ta ce ta kama ‘yan Pakistan ɗin – masu suna Asif Muhammed mai shekara 45, da kuma Hussain Naveed, mai shekara 57 – da laifin safarar koken da nauyinta ya kai kilo 2,985.5kg, a yayin da suke shirin hawa jirgi zuwa birnin Lahore na Pakistan.
Sanarwar ta ci gaba da cewa mutanen na da takardun izinin zama a Najeriya, waɗanda take zargin cewa na bogi ne, kuma suna yawan zuwa Najeriya da nufin yin kasuwancin atamfofi.
Emergency Digest
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1486 days 2 hours 19 minutes 38 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1468 days 4 hours 1 minute 3 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com