Shugabannin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU sun shiga ganawar sirri ta gaggawa.
An ruwaito cewa kungiyar ta shiga ganawar sirrin ne da tsakar ranar Litinin, a harabar sakatariyar kungiyar da ke jami’ar Abuja.
Ganawar karkashin jagorancin shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke, za ta duba batun biyan malaman rabin albashin watan Oktoba.
Read Also:
Tun da fari dai kungiyar reshen jami’ar Jos Sun dakatar da mambobin su da zuwa aiki har sai gwamnatin tarayya ta biya su cikakken Albashin su, duk da sun bayyana cewa ba yajin aiki suka shiga ba.
Sai dai daga bisani gwamantin Nijeriya ta Magantu kan biyan su ALbashin na kwanaki 17 da suka yi aiki a cikin su, duk da abinda kungiyar ta kira alkawarin gwamantin tarayya ta dauka musu na biyan su Albashin watan na Oktoba cikakken.
Idan dai za’a iya tunawa kugiyar malaman Jami’oin Nijeriya ta tsunduma yajin aiki ne bisa abinda ta kira gazawar gwamnatin kasar na gaza biya mata bukatun da ta nema, yajin aikin da suka kwashe watanni 8 ba tare da sun shiga ajujuwan sub a domin koyar da dalibai.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 13 minutes 0 second,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 54 minutes 25 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com