Shalkwatan Tsaron Najeriya ya wallafa sunaye tare da hotunan wasu kwamandojin ‘yan ta’addar da suka addabi arewa maso gabashi da kuma arewa maso yammaci da tsakiyar arewacin Najeriya.
Shalkawatan tsaron ta ce, zata bada tukuicin Naira miliyan 5 ga duk wani dan Najeriya da ke da bayanai kan yadda za a iya cafke ‘yan ta’addar.
wannan dai na wani bangare na daukar matakin ci gaba da aikin kakkabe mayakan dake tayar da kayar baya a yankunan. abin da ta bayyana mayin aikin daya rataya a wuyan ta maido da da zaman lafiya a yankunan.
Sunayen ‘yan ta’addar da ake nema ruwa a jallo kamar yadda darektan yada labaran shalkwatan tsaron Manjo Janar Jimmy Akpor ya fitar, sun hadar da:
SANI DANGOTE – daga kauyen Dumbarum, Karamar Hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
BELLO TURJI GUDDA – daga kauyen Dakai, jihar Zamfara.
LEKO – daga kauyen Mozol, jihar Katsina.
DOGO NAHALI – daga kauyen ‘yar tsamiya, Karamar Hukumar Kankara, jihar Katsina.
HALILU SUBUBU – daga kauyen Sububu a Karamar Hukumar Maradun, jihar Zamfara.
NAGONA – daga Angwan Galadima da ke ISA a jihar S|okoto.
Read Also:
NASANDA – daga kauyen Kwashabawa, Karamar Hukumar Zurmi, jihar Zamfara.
ISIYA KWASHEN GARWA – daga kauyen Kamfanin Daudawa da ke Faskari a jihar Katsina.
ALI KACHALLA da aka fi sani da ALI KAWAJE – daga kauyen Kuyambara a jihar Zamfara.
ABU RADDE – daga kauyen Varanda a Karamar Hukumar Batsari, jihar Katsina.
DAN-DA – daga kauyen Varanda a Karamar Hukumar Batsari, jihar Katsina.
SANI GURGU – daga kauyen Varanda a Karamar Hukumar Batsari, jihar Katsina.
UMARU DAN NIGERIA – daga kauyen Rafi da ke Mada a Gusau, jihar Zamfara.
NAGALA – daga Maru a jihar Zamfara.
ALHAJI ADO ALIERO – daga kauyen Yankuzo, a Karamar Hukumar Tsafe, jiharZamfara.
MONORE – daga ‘Yantumaki, jihar Katsina.
GWASKA DANKARAMI – daga kauyen Shamushele a Karamar Hukumar Zuri, jihar Zamfara.
BALERI – daga Karamr Hukumar Shinkafi, jihar Zamfara.
MAMUDU TAINANGE – daga kauyen baranda, Karamar Hukumar Batsari, jihar Katsina.
daga bisani shalkwatar ta ce ga dukkan mai wani karin bayani kan wadannan ‘yan ta’adda sai ya kira 09135904467 domin yin bayani.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 36 minutes 56 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 18 minutes 21 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com